Lokacin bazara lokacin aikin gona ne a kasar Sin. Yanzu haka a nan kasar, manoma na fama da ayyuka a cikin gonakinsu, tare da fatan ganin samun girbi mai armashi. Sai dai abin da ya fi jan hankali shi ne yadda suke amfani da kimiyya da fasahohin zamani wajen gudanar da ayyukansu. Misali a lardin Jiangxi da ke kudancin kasar Sin, injunan gona na zamani na samun karbuwa sosai, musamman ma injin dashen tsiron shinkafa marar matuki, wanda ke iya sarrafa kansa wajen dashen tsiron shinkafa bisa taswirar gonaki da tauraron dan Adam na Beidou ya samar masa. Sai kuma a lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin, ana amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI wajen tantance yanayin gonaki tare da ba da jagorancin gudanar da aikin gona.
A hakika, hakan ya faru ne sakamakon yadda kasar Sin ke ba ayyukan gona matukar muhimmanci. A farkon kowace shekara, takardar farko da kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta kan bayar dangane da muhimmiyar alkiblarta kusan ta kan shafi ayyuka masu alaka da gona da kauyuka da ma manoma. Ga shi a kwanan nan, an fitar da takardar ta bana, wadda ta tsara ayyukan da za a gudanar, hakan kuma, shekaru 22 a jere ke nan da takardar ke mai da batutuwan noma da kauyuka da manoma a matsayin jigonta.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Duba Ƙarin Farashin Wutar Lantarki
- Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Zaftare Albashin Ma’aikata
Abin lura shi ne, a karo na farko, takardar ta bana ta gabatar da manufar “raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona”, wadda ta tsara ayyukan da za a gudanar a fannonin nazarin irrai da inganta injunan gona da kuma bunkasa ayyukan gona na zamani. Lallai “raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona” na nufin amfani da kimiyya da fasahohin zamani wajen gudanar da ayyukan gona. A kasar Sin, ya zama dole a bunkasa ayyukan gona na zamani don samar da isasshen abinci ga al’ummar kasar da yawansu ya kai biliyan 1.4, musamman a yayin da ake fuskantar matsalolin karancin gonaki da kuma raguwar yawan manoma.
Raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona, ba kawai yana da ma’ana ga zamanantar da ayyukan gona a kasar Sin ba, haka kuma zai iya ba da muhimmin taimako ga kasashen Afirka wajen daidaita matsalolin abinci da talauci da ma zamanantar da kan su. A halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya na kara fuskantar matsalar samar da isasshen abinci, sakamakon matsalolin sauyin yanayin duniya da ma rikice-rikicen da ke faruwa. Ta hanyar raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona, kasashen Afirka za su iya kyautata kwarewarsu wajen samar da hatsi, tare da rage dogaro da shigar da abinci daga ketare, hakan zai taimaka ga tabbatar da samar da isasshen abinci. Ban da haka, raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona zai taimaka ga saukaka fatara a kasashen Afirka. Kasancewar sama da kaso 70% na al’ummar kasashen Afirka, musamman ma kasashen da ke kudu da hamadar Sahara, suna sana’o’i masu alaka da ayyukan gona, inganta ayyukan gona da kuma kara kudin shigar manoma na da matukar muhimmanci wajen daidaita matsalar talauci. Daga karshe, noma ya kasance ginshikin tattalin arziki a akasarin kasashen Afirka, don haka, raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona zai iya inganta ayyukan noma, wanda hakan zai sa kaimin bunkasuwar tattalin arziki baki daya.
Har kullum, noma wani muhimmin fanni ne na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. A ‘yan shekarun baya, hadin gwiwar ayyukan noma a tsakanin Sin da kasashen Afirka ya kara inganta bisa shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da ma tsarin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. Tuni kasar Sin ta kafa cibiyoyin nune-nunen fasahohin noma 24 a kasashen Afirka, tare da yayata fasahohin noma na zamani fiye da 300, matakan da suka sa amfanin gonar da aka samar a yankunan da abin ya shafa karuwa da kaso 30% zuwa 60%, wadanda kuma suka samar da alfanu ga manoma na magidanta sama da miliyan 1 a Afirka. A gun taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da ya gudana a watan Satumban bara a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da wasu matakai 10 na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wajen zamanantar da kansu, ciki har da matakin da ya shafi bunkasa ayyukan noma, kuma abin lura shi ne za a kafa kawancen kirkire-kirkiren fasahohin noma a tsakanin Sin da kasashen Afirka.
Akwai makoma mai haske wajen raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona, wanda tabbas zai taimaka wa Sin da kasashen Afirka wajen gaggauta zamanantar da ayyukan gona, har ma da zamanantar da kasashensu baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp