Shafin Taskira shafi ne da yake zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda Ramadan Basket ke tafiya a yanzu, duba da yanayin da al’umma ke ciki na tsananin rayuwa.
A kowacce shekara matasa samari na zage-damtse wajen ganin sun nuna bajintarsu ga ‘yan matan da suke so ko suke son aura, ta hanyar aika musu da kayan shan ruwa na-gani na-fada wanda suke kiransa da Ramadan Basket.
Sai dai kuma a wannan shekarar tsarin ya canja duba da yanayin halin rayuwa da al’umma suka tsinci kansu ciki, wanda dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin Taskira game da wannan batu; Ko ya Ramadan Basket ke tafiya a yanzu?, Wane abu ne ya fi damun samari da ‘yanmata game da Ramadan Basket?, Ya kuma batun kayan sallah da samari ke kaiwa ‘yanmatansu shin an fara kaiwa ko tukunna dai?
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Sa’adu Abdullahi Inuwa, Mallam madori A Jihar Jigawa:
Magana ta gaskiya wannan azumin bana mata sai dai su yi hakuri, domin matasa ba za su iya bada Ramadan basket ba domin ana cikin wani hali na kuncin rayuwa da tsadar rayuwa. Abin da ya fi damuna game da Ramadan basket din bana shi ne matsalar kudi da kuma tsadar kaya. Maganar gaskiya sai dai ‘yan mata su yi hakuri, domin samarin ma bana duk wanda ka gansa da shadda to ka jinjina masa domin bana yayin yadi za a yi saboda babu kudin siyan shadda. Ina kira zuwa gare ku samari da ‘yan mata da mu fidda rai a kan yin Ramadan Basket ga ‘yan matanmu domin gudun shiga wani hali na rayuwa. Ina bawa ‘yan uwana matasa shawara a kan su dage wajen neman na kansu kada mutum ya raina sana’a duk kankantarta mu yi domin ganin rayuwarmu ta inganta.
Sunana Rahma Ahmad, Jihar Kano:
Mu dai anan bangaren da nake gaskiya sai a hankali, samari sun yi shuru, kuma mu ma ‘yan mata ba mu tada hankalinmu ba sabida mun san halin da kasa take ciki, sai muna yi wa juna uzuri, amma ba a ma zancen wani Ramadan Basket. Ni babban abin da ya fi damuna shi ne; yadda wasu ‘yan matan suka mayar da Ramadan Basket kamar wani farilla duk halin da ake ciki mace kawai ita burinta a kawo ta yi fafa wajen kawaye, musamman in tanada kawar da ita saurayi ya kai mata. Shi ma kayan sallah har yanzu dai samari ba su fara bayarwa ba, anan gefenmu dai ni ban ji wata ta ce ga saurayinta ya kawo mata ba, kowa yana ta kai wa zai bi ka ta kayan sallah. Shawarar da zan bawa iyaye shi ne; su rangwantawa saari kar a ce dan saurayi bai kai Ramadan Baske ba, baya son yarinya a rika duba halin da ake ciki, kuma su daina saka ‘ya’yansu suna rokar saurayi kayan sallah, su ma samari dan Allah su daina takurawa kansu kan abin da ya fi karfinsu, su yi hakuri duk lokacin da suka samu sai su yi wa ‘yan matan. ‘Yan uwana mata ku daina fafa da karya dan kawai ku birge kawayenku da wasu mazan, a yi hakuri ko dan halin da ake ciki yanzu, Allah ya sa mu dace.
Sunana Alh. Aminu Garba Halliru:
Kusan ma yenzu in dai a ka yi la’akari da wannan rayuwar yenzu su kansu matan sun waye ba sa irin tambaya akan Ramadan basket saboda sun fahimci su kansu samarin ba sa san tambayar, saboda indai ki ka tambaya sai a nemi a yi rikici sai komai ya lafa sai a dawo dan barka da sallah ma a fasa bayarwa, kuma su ma ‘yan matan wasu suna bayarwa ga wanda yake bayarwa, amma mafi akasari suna hakan ne saboda a ramawa kura aniyarta. Abin da ya fi damuna shi ne abin da bai zama dole ba, kawai mu kago mu dorawa kanmu to ko inada niyyar yin Ramadan basket din sai na fasa saboda ba dole bane. Maganar gaskiya babu wannan maganar a wannan damanin saboda samarin yanzu ba su da kudi, kuma da dama basu shirya yin auren ba suke fadawa soyayya da ‘yan mata, sai ki ji suna cewa ai bai zo a hadisi ba, wani yana ganin azumi saura ‘yan kwanaki sai ya nemi kirkirar fada sai bayan sallah su dawo. Toh ni abin da zan ja hankalin samari shi ne ku daina karya dan a so ku, kayi bukatarka daidai yadda za ka iya, duk da kyautatawa a soyyaya babu aibu, amma ya kamata ka yi abin da za ka iya ba ka takura ba. Su kuma mata su daina tsammanin wani abu daga gurin samari saboda sa rai da ci shi ke kawo yunwa, kuma a rika hakuri da abin da aka samu. Shawarata anan shi ne; kowa ya tsaya yayi abu daidai yadda zai iya kar a rika la’akari da rayuwar wasu, domin Allah ya bawa kowa rabonsa samari su rika fadar gaskiya, kuma ‘yan mata su rika hakuri.
Zainab Zeey Iliyas Jihar Kaduna:
Wannan shekarar ana cikin wani yanayi da sai dai mu ce innalillahi wa inna ilaihirraji’un, amma fa ko ina hakan take wasu samarin sun yi wasu kuma ba su yi ba, amma mafi rinjaye su ne wanda ba su yi Ramadan Basket ba. Abin da ya fi damuna shi ne; yadda za ki ga mace tana fushi da saurayi karshe ma har ta kai da ta rasa shi sabida kawai bai kai mata komai ba, tai ta tashin hankalin da sai ya kai da saurayi ya daina sauraranta, madadin ta taya shi addu’a tare da al’ummar gari na halin da a ke ciki. Shawarata ga ‘yan mata dan Allah a rika a hakuri ba sai saurayi ya kaho komai ba, a tausayawa saurayi muddin ba shi da shi, amma dai idan yanada shi ya kamata shi ma saurayin ya kai wa budurwa ko yaya ne.
Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya yanayin da a ka samu kai a ciki a wannan wata mai alfarma na ramadan yanzu ba wai ta Ramadan Basket a ke ba duba da yadda aka samu kai a ciki halin tsadar rayuwa dama tsananin talauci, don haka wadanda suka yi wannan ihsani ga ‘yan mata a bana sune kadan, domin abincin da za a ci a ke faman nema. To abin da ya fi damu na game da Ramadan Basket shi ne yadda wasu ‘yan mata suka dauke shi kamar shi ne soyayya idan saurayi bai samu dama ya yi ba to suna ganin kamar ma baya son ta, wanda kuma ba haka bane yanayi ne na tsadar rayuwa da ma tsananin talauci da a ka samu kai a ciki ya jawo, wanda abinci ma yana yi wa al’umma wuya. To batun kayan sallah ma wani abu ne dan hali, domin yi wa budurwa kayan sallah ihsani kuma yana da kyau saurayi ya yi wa budurwa sa ihsani domin yana kara dankon soyayya a tsakanin saurayi da budurwa, to amma idan saurayi bai samu dama ba sai a yi hakuri a yi addu’ar Allah ya kawo mana saukin rayuwa. To kira na anan da samari shi ne su ji tsoron Allah su nemi halak a dage wajen neman abun rufa asiri idan har da dama to a yi wa ‘yan mata ihsani amma idan babu dama kar a tukurawa Kai, su ‘yyan mata su ma su ji tsoron Allah kar a tukurawa samarin wajen dole sai sun yi Ramadan Basket ko kayan sallah, domin hakan yana iya jefa samari cikin wani hali har ta kai ga sun koma sata. To shawarata a nan ita ce; matasa maza da mata kowa ya ji tsoron Allah, kuma a duba yanayin da a ke ciki idan har Allah ya bawa saurayinki dama ya yi miki Alhamdullilah idan ma bai samu dama ba to a yi masa addu’ar Allah ya buda masa a gaba zai yi in sha Allah, daga karshe nake addu’ar Allah ya kawo mana saukin rayuwa a kasar mu Najeriya da ma duniya baki daya.
Sunana Malama Rahama Musa, Dan zomo Sule Tankarkar A Jahar Jigawa:
Gaskiya a wannan yanayin da muke ciki an samu karancin Ramadan Basket, amma duk da haka samari sun taka rawar gani za ka ga koda bai hada kayan ba suna bada kudi daidai yadda Allah ya hore musu wasu kuma sun hada kayan kowa da yadda Allah ya hore masa. Abin da ya fi damuna a Ramadan Basket shi ne yadda wasu ‘yan matan suke ganin gazawar samarin su idan ba su yi musu ba. Batun kayan sallah gaskiya samari suna kokari shi ma kamar Ramadan Basket wasu suna hada kaya wasu kuma suna bada kudi daidai abin da Allah ya hore musu. Kiran da zan yi wa ‘yan mata da samari a nan shi ne; mata ku sani duk wannan abu da ake yi ba dole bane kuma kar ki bari shaidan ya sa ki ke ganin gazawar samarinku a kan kayan sallah ko Ramadan Basket, duba da yanayin da muke ciki. Samari, idan wannan al’adar ta taso ku rika kokari kuna farantawa ‘yan matanku ko kadan ne saboda su mata sunada wata dabi’a suna ganin idan irin wannan abu ya tashi saurayin bai mata ba tana ganin ma kamar ba da gaske yake son ta ba, su a tunaninsu yanzu samari ba sa son farantawa ‘yan matansu har sai sunada tabbacin za su aureta to wannan yake sa su ji shakku a kan soyayyarku. Amma idan kanada dama koda karamar kyauta ce hakan zai sa ta ji dadi kuma har ta yi alfahari da ita, dama ta san yanayin da ake ciki. Iyaye ku kula da halayyar yaranku ku nuna musu bata kayan sallah ko Ramadan Basket ake gane miji nagari ba, ‘yan mata a rage buri ba ki da gashin wance ba za ki yi kitson wance ba, Allah ya kawo mana wannan matsala ta tsadar rayuwa.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano, Karamar Hukumar Rano:
Gaskiya bana sai a hankali domin ba ma na jin wannan maganar a namu yankin. Rashin kudi da kuma tsadar abubuwan yau da kullum. Maganar kayan sallar bana sai hakuri maza da matan, domin ana ta abin da za a ci waye yake ta kayan salla sai dai hakuri da abin da ya sawwaka kawai. Kira na a nan shi ne ‘yan mata su yi hakuri duba da halin da ake ciki su bawa samari shawara idan ma saurayin yana kokarin takurawa kansa ya yi mata to ta bashi shawara ya taimaka a gidansu ko gidansa wajen kayan abinci da kuma dan abin da za a yi harkokin sallah da su. Shawarata a nan ita ce; samari su taimakawa iyaye da ‘yan uwa su bar ‘yan matan, duba da su ma sun san halin da aka tsinci kai a cikinsa yanzu. Allah kasa mu dace.
Sunana Umar Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:
Duba da yadda aka samu kai wannan lokacin Ramadan Basket bai samu wurin zama ba a wajen samari. Rashin kudi hade da tsadar rayuwa da a ka fuskanta a wannan shekarar. Na’am wasu samarin sun fara kun bura cikinsu sun kai duk da matsi da a ke fuskanta. Kira na shi ne; “yan mata su kauda Ido kan batun maganar Ramadan Basket. Shawarata ita ce su ‘yan mata su nemi abin dogaro da kai domin su daina jiran tsammani ga samari.
Sunana Hassana Sulaiman, Hadejia A Jihar Jigawa:
To Uhmmmm batun Ramadan Basket bana sai dai hamdala kawai za mu ce, dan kowa ganinsa ma yayi wuya ga samarin da suke kokarin kaiwa ‘yammatan nasu a bana dai, kuma batun kaiwa ramadan basket da samari ke yi kusan duk shekara idan azumi ya zo, wannan azumin kan ‘yan’matan dai basu gan shi ba sai dai sun ga bakin ido wasu kuma sun ga sakon katin waya ko data. To kusan abin da ya fi damun gameda ramadan basket ɗin nan shi ne yadda samari ke yawaita tsokanar ‘yammatan da batun nasa musamman ma a kafofin sada zumunta tare da wallafawar wasu kafofin suna tambaya hakan na damun mu gaskiya ‘yammatan. Oh idan kuma muka koma batun kayan sallah da samari ke kaiwa ‘yammatan nasu shi ma dai wannan karon wasu sun yi kokarin yin hakan na badawa koda baida yawa, wasu kuma sai dai batun hakuri wannan karon dan babu ma zancen kawo wa kadan duk wanda ta matsa da batun to fa batawa da saurayin za su yi sai kuma bayan sallah ya dawo kan. Ƙiran da za mu yi wa juna kuma kowanne bangaren na samarin da ‘yammatan akan batun ramadan basket ɗin nan shi ne kowa daga cikin masoya ayi hakuri da wannan yanayin da muka tsinci kanmu a cikin sa, mu yi hakuri da maganar sa ma dai mu ga zuwa gaba wani lokacin indai komai yayi daidai za a yi abin da yafi ramadan basket ma ,kuma matuƙar soyayya ta gaskiya ce dan ba’a yi ramadan basket ba babu ta yadda za’a rabo akan ba’a bayar ba .
Sunana Hamza Rabiu (Abba Alhaji), Maalam Madori A Jihar Jigawa:
Ramadan Basket wata sabuwar al’ada ce wacce samari suke yi wa ‘yan matansu a lokacin mafi yawancin samarin suna kashe makudan kudade domin su burge ‘yan matan nasu, mafiya yawan samarin su kan saka abubuwa kamar haka; Madara, bonbita, Neskofin, da sauran abubuwan more rayuwa, amma mafi yawancin yanzu sakamakon halin da ake ciki na tsadar rayuwa mafi yawancin samarin basu yi wa ‘yan matan nasu wannan dabi’ar da suka dauka ta Ramadan Basket ba, ma fi yawanci samari ne suke kaiwa ‘yan matan nasu amma suma ‘yan matan suna kaiwa samarin nasu wannan kyautar ta Ramadan basket amma mafiya bada wannan kyautar samari ne suke hadawa ‘yan mata. A gaskiya abun da ya fi damuna game da wannan al’adar ta Ramadan Basket mafiya samarin da suke bada wannan kyautar basu da kyakyakyawar sana’ar da idan an ce a fito a yi aure ba sa iya futowa, haka zalika suna takura kansu ne domin su tara kudin nan ko kuma abokan su ne suke hada musu kwantibushin domin siyan kayan Ramadan Basket, hakan ya kan sana sawa mutuwar zuciya. Maganar batun kayan sallah da samari suke hadawa ‘yan matan nasu yanzu haka sakamakon halin tsadar rayuwar da ake ciki samari ba sa iya hadawa ‘yan matansu kayan sallah, amma wasu daga ciki suna iya siyawa ‘yan mata kayan sallah amma saboda tsadar rayuwar ba sa iya siya musu komai kamar a shekarar da muka yi bankwana da ita a halin yanzu samari wasu daga cikin samarin sun fara kaiwa ‘yan mata kayan sallah amma wasu daga ciki ba sa iya siyawa ‘yan matan nasu kayan sallah. A gaskiya Kiran da zan yi game da wannan kyautar da samari suke hadawa ‘yan matan nasu ta Ramadan basket Kiran da zan yii ya kamata samari su duba halin da ake ciki su daga kafa wajen hada kayan Ramadan Basket duk da cewa duk mace da kace kana sonta itama tana sonka an kulla alaka mai kyau haka zalika ita ma kyautar da samari suke bawa ‘yan matansu ta kayan sallah yana daya daga cikin kyautatawa amma samari sukan takura kansu wajen hada kayan sallah. Shawarar da zan bawa ‘yan uwa na mata da maza musamman ma ‘yan’uwa na maza a duba rayuwar da ake ciki a rage wannan bajintar ake hadawa ‘yan mata haka kuma iyaye su dinga duba a lakar data ke tsakanin samari da kuma ‘yan mata wasu daga cikin samarin su kan iya fakewa da bada wannan kyautar don su lalatawa ‘yan mata rayuwar su daga karshe sai a yi dana sanin sakarwa samari fuska wajen karbar wannan kyautar daya bawa buduwar tasa.