Tun bayan kammala zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP ake ta samun zaman doya da manja a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar PDP.
Wani sabon rikici ya kunno kai a kan zabin dan takarar mataimakin shugaban kasa a Jam’iyyar PDP.
- Bincikenmu: An Dade Da Hana Karuwanci A Neja, Amma Abin Ya Dau Sabon Salo
- Da Hannun Amurka A Kuskuren Kai Harin Sojin Nijeriya Na 2017 A Borno — Bincike
Akwai rahotanni da suke cewa Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, yana barazanar ficewa daga PDP bayan da Atiku Abubakar ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.
Wadannan rahotannin ne ya sanya wasu ke ta kamun kafa a wajen Wike idan ya bar jam’iyyar PDP ya shiga jam’iyyarsu ganin irin tasirin da yake da shi a yankin kudu maso kudancin Nijeriya.
Wasu fitattu manyan jam’iyyar PDP sun fito suna kokarin cire wa dan takarar shugaban kasar zani a kasuwa, inda suke cewa bai kyauta ba da ya tsallake gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, wajen zaben abokin takarasa, alama ce ta yankan shakku cewa za su kunna wata wutar rikici, wadda idan ba a yi wa tubkar-hanci ba za ta cinye jam’iyyar.
A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, a wata zantawa da ‘yan jarida ya ce sam-sam dan takarar shugaban kasar a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Ababukar, bai yi halacci ba da ya ki amincewa da Gwamna Wike a matsayin mataimakisa.
A hannu guda kuwa, wasu ‘yan takarar shugaban kasa da kusoshin wasu jam’iyyun hamayyar ke tururu zuwa wajen Wike, kuma ga dukkan alamu da nufin yin wuf da shi daga jam’iyyar PDP.
A kwanakin nan an ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya kai wa Mista Wike ziyara.
An ga kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci gwamnann Ribas.
Haka kuma wasu gwamnonin APC sun gana da Wike.
Kafafen yada labarai dai da dama sun ruwaito cewa cikin gwamnonin sun hada da gwamnan Jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnoni, Dakta Kayode Fayemi tare da gwamnan Legas da kuma na Ondo.
Sai dai babu wani abu da ya fito na dalili da kuma sakamakon tattaunawar tsakanin Wike da gwamnonin na APC, amma ba ya rasa nasaba da zaben 2023.
Baya ga wannan kuma, sai ga ‘yan tawayen APC wato su Yakubu Dogara da Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal sun kai wa Wike ziyara jim kadan bayan dawowarsa daga bulaguro a kasar waje.
Har Yakubu Dogara yake cewa Nijeriya na bukatar mutane irin su Wike don a gyarata.
A ranar Lahadi, 31 ga watan Yulin 2022, gwamnonin PDP sun kai wa Wike ziyara. Gwamnonin sun kai ziyarar ce kwana daya bayan da manyan ‘yan tawayen APC, suka Kai masa ziyara.
Gwamnonin da suka kai wa Wike ziyara, sun je ne tare da wasu tsoffin gwamnonin PDP, inda a ranar Lahadi suka gana da shi a asirce, a gidan Gwamnatin Jihar Ribas da ke Asokoro cikin garin Abuja.
Ba a san dai abin da suka tattauna ba. Amma kuma tabbas tattaunawar ba ta rasa nasaba da sabanin da ke kara tsanani tsakanin Wike da Atiku Abubakar.
Daga baya Wike ya ce Atiku ya yaudare shi, domin bayan kammala zaben, ya bi Wike har gida ya ba shi hakuri. Kuma ya ce shi zai dauka mataimakin takararsa.
Manyan PDP sun fara jin tsoron Wike tun bayan da gwamnonin APC uku daga kudu maso yamma suka kai masa ziyara.
Sai kuma ziyarar da Yakubu Dogara da Babachir Lawal suka kai masa a ranar Asabar.
Rahotanni dai da dama na nuna cewa Wike dai na cewa ba zai fita daga PDP ba, shi da jam’iyyar mutu-ka-raba.
Amma abun tambaya a nan wani irin tasiri Wike yake da shi haka har zama tamkar gwal?
Lallai wannan tambaya tana da amsa, idann aka duba irin tasirin da yake da shi a cikin harkokin siyasar Jihar Ribas da ma Nijeriya gaba daya za a ga cewa rasa irin Wike a cikin jam’iyya babban nakasu ne, domin yana da dimbin magoya baya, sannan yana iya amfani da kudinsa wajen gina jam’iyya da samun nasara a cikin siyasa.
Ya kasance wani bango da ake kallo a cikin harkokin siyasan kudancin Nijeriya da ke da tasiri wajen tsayawa kan akidarsa, wanda yake da wahalar taukwaruwa.
Tabbas Wike yana da matukar tasiri a cikin harkokin siyasar Nijeriya, musamman ma a cikin jam’iyyarsa ta PDP.