ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Amurka Ke Goyon Bayan Matakin Japan Na Zuba Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku?

by CMG Hausa
2 years ago
Amurka

A daidai lokacin da kasashen duniya ke yin Allah wadai da yadda gwamnatin kasar Japan ta kare aniyarta ta zubar da ruwan dagwalon nukiliya na tashar nukiliya ta Fukushima cikin teku, jakadan kasar Amurka a Japan Rahm Emanuel ya yi tattaki zuwa Fukushima, inda ya nuna yadda ya ci abincin teku na wurin, don bayyana goyon baya ga matakin da Japan ta dauka na zubar da ruwan cikin teku. Amma da gaske ne Amurka ba ta damu da illolin da matakin na Japan ka iya haifarwa? 

Alkaluman da ma’aikatar kula da aikin gona da dazuzzuka da albarkatun ruwa ta kasar Japan ta fitar sun shaida cewa, Amurka ta kasance kasar da ta fi yawan rage shigowa da kayayyakin ruwa daga kasar Japan tun farkon bana, musamman ma wasu nau’o’in abincin teku da suka fito daga yankin da ruwan dagwalon nukiliya ya fi shafa. Da haka, muna iya gano cewa, gwamnatin Amurka na sane da illolin da matakin ka iya haifarwa. To, ke nan me ya sa Amurka ta nuna hakuri har ma ta goyi bayan Japan ?

  • Sakon Shugaban Kasar Sin Ya Nuna Makomar Aikin Raya Tattalin Arziki Mai Alaka Da Fasahohin Zamani

A hakika, matsayin da Amurka ke dauka kamar ciniki ne take yi da Japan, inda ta hanyar bayyana goyon baya da fahimta, Amurka ke taimakawa Japan wajen tinkarar kyama da shakku da ake nuna mata, yayin da Japan a nata bangare, ta kara ba Amurka hadin kai wajen aiwatar da shirye-shiryenta a duniya. A hakika, a cikin shekaru biyu da suka wuce, Japan ta yi ta kokarin ba da hadin kai wajen aiwatar da tsarin tattalin arziki a kasashen dake yankin tekun Indiya da fasifik wato Indo-Pacific da Amurka ke jagoranta.

ADVERTISEMENT

Amurka wadda a kullum ke ikirarin mai rajin kare muhalli, amma ainihin abin da take kulawa ba muhallin duniya ba ne, illa ci gaba da yin babakere a duniya.

Makonni biyu ke nan da Japan ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku, kuma hakan zai ci gaba nan da shekaru 30 zuwa 40 masu zuwa. Wani nazarin da jami’ar Tsinghua ta kasar Sin ta yi ya shaida cewa, da farkon fari, kasashen da ke yammacin tekun Pasifik ne za su fi fuskantar illolin da matakin zai haifar, amma sakamakon igiyar ruwa, nan da shekaru 10 masu zuwa, yankin Amurka da ke gabashin tekun za su fuskanci tarin sinadarai masu guba da suka ninka na mashigin teku na Japan har sau uku.

LABARAI MASU NASABA

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

Abin takaici shi ne, ‘yan siyasa na Amurka sun fi mai da hankali a kan cimma moriyarsu ta yanzu, babu ruwansu da matsaloli da gwamnati ta gaba za ta fuskanta. (Mai zane: Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko
Daga Birnin Sin

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

November 14, 2025
Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya
Daga Birnin Sin

Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya

November 14, 2025
Next Post
Zamfara

Dusa Muke Ci Muke Rayuwa Saboda Tsananin Rashin Tsaro - Mazauna Wani Yankin Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa

November 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

November 14, 2025
BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani

BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani

November 14, 2025
Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya

Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya

November 14, 2025
Sin Ta Yi Tsokaci Kan Kalaman Da Firaministar Japan Takaichi Sanae Ta Yi A Kanta

Sin Ta Yi Tsokaci Kan Kalaman Da Firaministar Japan Takaichi Sanae Ta Yi A Kanta

November 14, 2025
Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

November 14, 2025
ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027

ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027

November 14, 2025

Rikicin PDP: Fiye Da Wakilai 3,000 Ne Za Su Raba Gardama A Babban Taron Jam’iyyar

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.