Kwanaki kaɗan bayan kama aiki a ƙungiyar Bayer Leɓerkusen, tsohon mai horas da Manchester United Eric Ten Hag ya gaza jagorantar ƙungiyar na tsawon ko da mako 10.
Ba mako 10 ba ma, ko mako 9 bai cika ba, inda ya yi kwana 62 kacal a ƙungiyar, bayan buga wasan gasar Bundesliga biyu kacal. An kore shi ne bayan Leɓerkusen ta gaza yin nasara a karawarta da Werder Bremen a ranar Asabar. Da farko Leɓerkusen ce ta shige gaba da ci 3-1, inda Bremen ta samu jan kati, amma daga baya aka tashi wasan canjaras 3-3.
- Al Hilal Za Ta Biya Yuro Miliyan 53 Don Ɗaukar Nunez Daga Liverpool
- Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar
Hakan ya biyo bayan kashin da Leɓerkusen ta sha a gida a hannun Hoffenheim a wasanta na farko na gasar Bundesliga na wannan kaka. Wasa ɗaya ne kacal Ten Hag ya samu nasara a matsayin mai horas da Leɓerkusen.
An naɗa Ten Hag a muƙamin ne a ƙarshen watan Mayu domin maye gurbin tsohon kocin ƙungiyar Ɗabi Alonso, wanda ya koma Real Madrid. Da farko, Leɓerkusen ta yi tsammanin zai iya jan ragamar sake gina ƙungiyar bayan rasa ƴan wasanta irin su Florian Wirtz da Jonathan Tah.
To sai dai sakamakon wasannin farko-farko na wannan kakar ba su yi kyau ba, amma ba wannan ne babban dalili ko kuma ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka haifar da korar Ten Hag ba. Kusan tun farko Ten Hag ya fara shafa wa kansa baƙin fenti sanadiyyar wasu matakai da ya ɗauka da kuma halayyarsa.
Misali, ya sauya lokacin da aka tsara yin wasan sada zumunta da ƴan ƙasa da shekara 20 na ƙungiyar Flamengo a lokacin da Leɓerkusen ta je atisaye a Brazil. An buga wasan kwana biyar kafin ranar da aka tsara tun farko, inda Leɓerkusen ta sha kashi da ci 5-1.
Haka nan a kusan wannan lokacin ne Ten Hag ya yanke hukunci kan batun tafiyar Granit Ɗhaka, inda ya ce ya kamata ya tsaye saboda Leɓerkusen ta rasa manyan ƴan wasa da yawa.
Sai dai tuni ƙungiyar ta sanar cewa Ɗhaka zai iya tafiya idan aka samu tayi mai kyau. Daga baya ya tafi Sunderland. Haka nan kuma Ten Hag ya soki ƴan wasansa tare da cewa ba su da kuzarin da ya kamata duk da cewa shi da tawagarsa ne suka jagoranci tawagar.
Bugu da ƙari an zargi Ten Hag da rashin kwarjinin da ake koci ke buƙata domin jan ragamar babbar ƙungiya, musamman ma ƙungiyar da ta kawo sabbin ƴan wasa da dama.
Za a iya cewa da alama ya riƙa shan wahala wajen shawo kan ƴan wasa su bi tsarinsa, domin wasu majiyoyi sun ce bai iya yi wa ƴan wasa wata ƙwaƙƙwarar huɗuba gabanin buga wasa. Sannan an bayyana cewa bai yi wa ƴan wasan jawabi ba gabanin karawarsu ta farko da Hoffenheim. Akasin Alonso, wanda aka ce shi ya riƙa ƙarin ganin ya ƙara ƙwarewa a harshen Jamusanci tare da samun ƙarin gogewa lokacin da yake jagorantar ƙungiyar ta Leɓerkusen.
Abin ya ba da mamaki sosai yadda shugabannin Leɓerkusen suka yanke shawarar korar Ten Hag da wurwuri haka domin wannan ba abu ne mai alfanu ba ga daraktan wasanni na ƙungiyar Simon Rolfes – wanda ya dage kan a ɗauki Ten Hag a lokacin da ƙungiyar ke son ɗaukar sabon koci a watan Mayu – har ma da shugaban ƙungiyar Fernando Carro.
A ƴan shekarun da suka gabata Ten Hag ya kasance ƙwararren mai horaswa lokacin da ya samu nasara sosai a Ajaɗ. Ya lashe gasar Holland sau uku sannan ya kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar zakarun nahiyar Turai ta Champions League a shekara ta 2019.
Ko a shekarar farko na jagorancin Manchester United aikinsa ya yi kyau babu laifi, kuma an alaƙanta barin aikinsa daga ƙungiyar kan rikicin da ƙungiyar ta fuskanta amma ba domin gazawarsa a matsayin mai horaswa ba. Amma a yanzu Leɓerkusen da alama tana cikin ruɗani. Kusan za a iya cewa a shirye suke su sayer da duk wani ɗan wasa da ya nuna aniyar barin ƙungiyar. A lokaci guda kuma ƴan wasa irin su Malik Tillman da Jarell Ƙuansah sun tafi ƙungiyar tare da sa ran cewa Ten Hag ne zai ci gaba da horaswa.
A yanzu Leɓerkusen na buƙatar nemo wanda zai maye gurbinsa. Akwai rahotannin cewa sun tattauna da tsohon kocin Barcelona Ɗaɓi, haka nan kuma tsohon mai horas da Dortmund da Leipzig Marco Rose na cikin waɗanda ake ganin za su iya samun aikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp