Mataimakiyar sakataren harkokin wajen kasar Wendy Sherman da kwamdan rundunar sojin kudancin Amurka ta (USSOUTHCOM) Laura Richardson, sun ziyarci Argentina a baya-bayan nan. Kuma yayin tattaunawarsu da jami’an Argentina, sun ambaci tasirin Sin a yankin Latin Amurka tare da gargadin Argentina da ta yi taka-tsantsan wajen raya huldarta da Sin.
Ba Wendy Sherman da Laura Richardson ne kadai jami’an Amurka da suka je Argentina a kwanan nan ba. Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa, alamu sun nuna cewa, Amurka na bibiyar dangantakar da Sin ke da ita a yankin Latin Amurka, musamman ma dangantakarta da Argentina.
- Kasar Sin Ta Soki Amurka Bisa Kakabawa Wasu Kamfanoninta Takunkumi Dangane Da Batun Maganin Fentanyl
Mene ne dalilin Amurka na yin hakan? Bisa nazarin kafofin watsa labarai na Argentina, tun bayan da ya kama aiki, shugaban Amurka Joe Biden ke karfafa manufofin magabacinsa na kokarin danne ci gaban kasar Sin, haka kuma ba ya burin ganin tasirin kasar Sin a Latin Amurka ko duniya.
Argentina babbar kasa ce a Latin Amurka. A ganin Amurka, dangantakar Argentina da kasar Sin na kalubalantar muradunta, kuma tana yi wa ra’ayinta na babakere barazana, don haka take yin dukkan mai yiwuwa na ganin ta katse ko kawo wa dangantakar tsaiko.
Amma abubuwa sun sauya a yanzu. Kasashen Latin Amurka na muradin hadin kai da hadin gwiwa da ma ci gaba, kuma yunkurinsu na neman ‘yanci na karuwa. A karshen karni na 19, tsohon shugaban kasar Mexico, Jose de la Cruz Porfirio Diaz Mori, ya taba furta cewa, kasarsa ta yi nesa da ubangiji, amma tana da kusanci da Amurka. Abun da ke faruwa yanzu a Latin Amurka ya tabbatar da ra’ayin kafofin watsa labarai na Argentina, wato, “Yayin da kasashe masu tasowa ke kokarin samun ci gaba, Latin Amurka na iya sauya tarihinta na kusanci da Amurka”. (Fa’iza)