“Wurin da ya fi kasar Sin kyau a nan gaba, shi ne kasar Sin ta nan gaba.” Kwanan baya, shugaba Xi Jinping ya ambato wannan ra’ayin rukunonin masana’antu da kasuwanci cikin jawabinsa, yayin halartar tarukan kungiyar APEC a San Francisco ta kasar Amurka, lamarin da ya ja hankalin duniya.
Me ya sa rukunonin masana’antu da kasuwanci na kasa da kasa suka zabi kasar Sin? Manufofi 3 da shugaba Xi ya jaddada a yayin tarukan APEC, wadanda kasar Sin ba za ta sauya ba, sun ba da amsa.
- Ana Fatan Sakamakon Ganawar Xi Da Biden Zai Taka Rawa Wajen Kyautata Dangantakar Sin Da Amurka
- Wang Yi Ya Tattauna Da Takwarorinsa Na Kasashen Larabawa Da Na Musulmi
Kasar Sin, inji ne mafi girma dake ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya. Gudummawar da za ta bayar kan bunkasar tattalin arzikin duniya a bana za ta kai kashi 1 cikin kashi 3. A ‘yan kwanankin baya, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya kyautata hasashen da aka yi kan karuwar GDP din kasar Sin a shekarar 2023 zuwa 5.4%. Hakan ya tabbatar da cewa, kasar Sin na da karfin juriya da boyayyen karfi, da dabaru da dama wajen raya tattalin arziki, kana tubalin tattalin arzikin Sin na samun ci gaba ba zai sauya ba.
Har ila yau, cikin manyan abokan cinikayyar kasar Sin guda 10, wasu 8 na cikin kungiyar APEC, haka kuma, kasar Sin ta kasance abokiyar ciniki mafi girma ga rukunoni 13 na kungiyar APEC. A yayin tarukan APEC a bana, kasar Sin ta gabatar da wasu sabbin matakan kara azama kan bude kofa ga ketare, ciki had da rika kyautata tsarin kare hakkin baki ‘yan kasuwa na zuba jari, ci gaba da rage abubuwan da aka tanada cikin jerin sana’o’i da ayyukan da aka haramta zuba jari kansu, yin adalci tsakanin baki da ‘yan kasar a fannin zuba jari kan kamfanoni da dai sauransu. Lamarin ya nuna cewa, kasar Sin ba za ta sauya aniyarta ta samar da yanayin kasuwanci da ya kai mizanin kasa da kasa wanda zai dace da bukatun kasuwa kuma bisa doka ba. Kana ba za ta sauya manufarta ta yin adalci a tsakanin baki da ‘yan kasar wajen samun kyakkyawar hidima ba.
Lallai wadannan manufofin 3 da kasar Sin ba za ta sauya ba, sun samar da tabbaci da kwanciyar hankali, wadanda duniya ke matukar bukata yayin da take fuskantar sauye-sauye da rashin kwanciyar hankali. (Tasallah Yuan)