• English
  • Business News
Friday, September 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Zai Faru Idan Iran Ta Datse Mashigar Hormuz Sanadiyar Hare-Haren Isra’ila?

by Mairo Muhammad Mudi
3 months ago
in Kasashen Ketare
0
Me Zai Faru Idan Iran Ta Datse Mashigar Hormuz Sanadiyar Hare-Haren Isra’ila?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Musayar wuta da ake yi tsakanin Isra’ila da Iran ta jawo fargabar yiwuwar Iran ta datse hada-hadar jiragen ruwa a mashigar Hurmuz, wanda shi ne hanyar dakon man fetur mafi muhimmanci a duniya.

Kusan kashi biyar na danyen man da ake amfani da shi a duniya yana bi ta mashigar ne mai girman kilomita 40.

  • Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin Sun Samar Da Sabuwar Hanyar Sufuri Ga Al’Ummun Kasashen Shiyyar Tsakiyar Asiya
  • Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (6)

Iran za ta iya daukar matakin hana wucewa ta mashigar, kamar yadda kwamandan rundunar sojin ruwa na kasar Iran ya bayyana.

Tsohon shugaban hukumar leken asirin Birtaniya wato M16, Sir Aled Younger ya shaida wa BBC cewa daga cikin manyan matsalolin da yakin zai haifar akwai datse tekun. “Datse tekun zai haifar matsalar tattalin arziki mai girma saboda yadda zai shafi farashin man fetur.”

Yawan fetur da ake jigila ta tekun

Labarai Masu Nasaba

Birtaniya Ta Amince Da Kafa Falasɗin A Matsayin Ƙasa

An Cafke Bature ÆŠan Shekara 37 Kan Mutuwar ÆŠan Nijeriya Mazaunin Birtaniya

Hukumar kididdigar makamashi ta Amurka US Energy Information Administration (EIA) ta kiyasta cewa a farkon shekarar 2023 an yi dakon kusan ganga miliyan 20 na fetur a a kullum ta tekun.

Wannan ke nufin ana kasuwancin kusan dala biliyan 600 na makamashi duk shekara ta tekun.

Duk wani tsaiko a tekun zai iya jawo matsala a hada-hadar man fetur a duniya, wanda nan take za a iya gani ta hanyar tashin farashin man.

Sai dai masana suna gargadin cewa daukar wannan matakin zai iya zafafa rikicin na Isra’ila da Iran.

Wannan kuwa shi ne zai jawo wasu kasashen cikin rikicin, ciki har da Amurka, wadda take ta’allaka da man fetur daga kasashen Larabawa.

Yaya girman mashigar Hormuz?

Mashigar Hormuz na tsakanin Iran da Oman ne. Tekun na da fadin kilomita 50.

Taswirar tekun ta nuna bangarorin da suke da kyau a tsaya, da wuraren da ba a so a tsaya da kuma tudun mun tsira a tsakanin bangarorin biyu.

Idan tankokin mai za su wuce, sai su wuce ta kusa da tsibirin Greater da Lesser Tunb – inda ake takun-saka tsakanin Iran da kasashen Larabawa kan mallakinsa.

Masana sun ce yaki na cikin abubuwan da suke jawo tsaiko a hada-hada ta mashigar kamar yadda ya faru a yakin Iran da Iran a shekarar 1980 zuwa 1988.

Amfani da tekun domin kare kai?

Masana sun ce a wajen Iran, datse hada-hada a mashigar Hormuz na nufin amfani da wata dama domin kare kanta.

Kamar yadda kasashen duniya suka dade suna adawa da yunkurin Iran na samun nukiliya, manyan kasashen duniya sun sha nanata cewa ba za su bari Iran ta yi amfani da tekun ba wajen shake duniya game da samun makamashi.

Masana sun yi hasashen cewa Iran za ta iya datse mashigar na wani dan lokaci. Amma wasu na ganin Amurka da kawayenta ba za ta bari hakan ya dauki lokaci ba, inda suke hasashen Amurka za ta iya amfani da karfin soji wajen bude mashigar.

Ta yaya Iran za ta iya datse mashigar Hormuz?

A wani bincike da cibiyar bincike ta Congressional Research Serbice ta Amurka ta nuna, ta ce Iran za ta iya daukar matakin a hankali. Hanyoyin sun kunshi:

Sanar da hana sufurin jiragen ruwa ba tare da bayyana hukuncin saba dokar ba

Sanar da tantance jiragen dakon man ko kuma kwacewa

Yin barin wuta kan jiragen dakon

Kai farmaki kan wasu jiragen dakon

Binne wasu nakiyoyin ruwa a tekun

Kai farmaki kan wasu jiragen kasuwanci da na soji

A yakin Iran da Irak, Iran ta yi amfani da makamin Silkworm domin kai farmaki kan tankokin man fetur, sannan ta dasa nakiyoyi a cikin teku.

Daya daga cikin nakiyoyin ne ya fasa jirgin USS Samuel B Roberts, wanda ya sa Amurka ta mayar da martani.

Sai dai duk da haka Iran ba ta datse mashigar ba baki daya, amma ta kara harajin shige da fice, sannan taa lafta wasu ka’idoji da suka jawo cunkuson jirage wajen ficewa daga gabar tekun.

Ƙarfin sojin Iran

Kwana biyu kafin harin Isra’ila da ya kashe kwamandan dakarun juyin juya-halin Iran Manjo Janar Hossein Salami, kwamandan ya ziyarci sashen sojin ruwa da ke aiki a mashigar.

Ya bayyana yankin tekun a matsayin daya daga cikin muhimman yankunan kare kai da kasar ke da su.

Ya bayyana jirgin da zai iya tafiya tsawon kilomita 10 cikin minti uku a yankin.

Janar Salami ya ce za su yi amfani da manyan makaman masu cin dogon zango domin kare kasarsu. Ya kuma ce za su yi amfani da nakiyoyin ruwa.

Salami ya ce za su fadada ayyukan jirage maras matuka.

Me masana suke hasashe?

Masana suna hasashen daya daga cikin hanyoyin da Iran za ta bi domin datse dakon kusan jirage 3,000 da suke wucewa ta tekun a kusan duk wata ita ce dasa nakiyoyi da amfani da jirage masu cin dogon zango domin kai farmaki kan jiragen.

Sojojin Iran da dakarun juyin juya-hali na kasar za su iya kai farmaki kan jiragen dakon man kasashen waje.

Sai dai kuma Amurka da Isra’ila za su iya kai farmaki kan manyan jiragen ruwan soji idan Isra’ila suka yi amfani da su.

Yanzu haka kafar bibiya harkokin tekun kasar da ke amfani tauraron dan’adam sun nuna jiragen yakin Iran a yankin kudancin kasar.

Wadanne kasashe ne za su fi shiga cikin tasku?

Binciken da masana daga cibiyar Borteda suka yi ya nuna cewa Saudiyya tana fitar da danyen mai kusan ganga miliyan 6 a kullum ta Hormuz – sama da duk wata kasa a yankin.

China da India da Japan da Koriya ta Kudu na cikin manyan kasashen da sufurin danyen man fetur ta tekun.

EIA ta kiyasta cewa a 2022, kusan kashi 82 na danyen man fetur da ake dakonsa ta mashigar, kasashen Asia ake zuwa da su.

A ranar 16 ga watan Afrilun 2025, kwana uku kafin Isra’ila ta kai hari kan tsaron sararin samaniyar Iran, kamfanin dillancin labaran Iran IRNA ya ruwaito shugaban Afirka ta Kudu Yoon Suk-yeol ya ce kashi 60 na man fetur din kasar na biyowa ne ta mashigar Hormuz.

Haka kuma EIA ta ce Amurka na shigo da kusan ganga 700,000 na danyen mai ta mashigar a kullum – kimanin kashi 11 na man da take shigo da shi, kuma kashi uku da man da take amfani da shi a kasar.

kasashen turai baki daya ba sa shigo da fetur da ya haura sama da ganga miliyan 1 a kullum.

Don haka, kasashen Larabawa da Asia ne za su fi fuskantar kalubale idan aka datse mashigar, sama da Amurka da turai da suke da alakar siyasa da Isra’ila.

Sannan akwai kasashen Asia da dama da suke da alaka mai kyau da Iran.

Rawar da China za ta taka

China na cikin kasashen da suka fi amfani da man fetur da ake jigila ta Hormuz. Iran na sayar da mai a farashi mai rahusa, kasa da farashin kasuwannin duniya, wanda hakan ya sa kasar ke samun sauki kan takunkumin tattalin arziki da Amurka ta kakaba mata.

Saboda yadda take matukar amfani da man fetur, China ba za ta yi maraba da duk wani abu da zai jawo tashin farashin mai ba, ko kuma samun tsaiko a dakonsa. Wannan ya sa China za ta yi amfani da diflomasiyya wajen hana yiwuwar daukar wannan matakin.

Akwai wata hanya daban bayan tekun?

Saboda barazanar da ake yawan fuskanta ta datse mashigar a shekarun da suka gabata ne ya sa kasashen da suke dakon man fetur a yankin suka samar da wata hanyar daban.

Wani rahoton EIA ya ce Saudiyya ta fara amfani da bututun gabas maso yammaci mai nisan kilomita 1,200, wanda za a iya tura ganga miliyan 5 a kullum.

A shekarar 2019, Saudiyya ta gyara wasu bututun gas domin su yi daukar danyen man fetur.

Hadaddiyar Daular Larabawa ta hada gabar tekunta na tudu da gabar Fujairah da ke gabar Oma da bututun da zai iya daukar gangan mai miliyan 1.5.

A watan Yulin 2021, Iran ta kaddamar da bututun Greh-Jask, wanda zai iya jigilar mai zuwa gabar Oman. Yanzu haka bututun zai iya daukar ganga 350,000 a kullum.

Rahoton EIA ta kiyasta cewa wadannan hanyoyin za su iya jigilar ganga miliyan 3.5 a kullum – kusan kashi 15 na man da ake jigila ta tekun a kullum.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AmurkaIranIsra'ila
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kiran Gwamnatin Tarayya Ga ‘Yan Jarida: Ku Zama Jigo Wajen Gina Dimokuraɗiyyar Nijeriya

Next Post

Hikimar Yunƙurin Sake Farfaɗo Da Noman Filanten A Jihar Nasarawa

Related

Birtaniya Ta Amince Da Kafa Falasɗin A Matsayin Ƙasa
Kasashen Ketare

Birtaniya Ta Amince Da Kafa Falasɗin A Matsayin Ƙasa

5 days ago
An Cafke Bature ÆŠan Shekara 37 Kan Mutuwar ÆŠan Nijeriya Mazaunin Birtaniya
Kasashen Ketare

An Cafke Bature ÆŠan Shekara 37 Kan Mutuwar ÆŠan Nijeriya Mazaunin Birtaniya

2 weeks ago
Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)
Kasashen Ketare

Makaman Rasha Masu Gudun Walkiya Da Ke Yi Wa Ƙasashen Turai Barazana

3 weeks ago
Girgizar Ƙasa Ta Kashe Sama da Mutune 600 A Afghanistan
Kasashen Ketare

Girgizar Ƙasa Ta Kashe Sama da Mutune 600 A Afghanistan

4 weeks ago
Ƴansandan Libya Sun Kama Ƴan Nijeriya Biyu Kan Zargin Fashi
Kasashen Ketare

Ƴansandan Libya Sun Kama Ƴan Nijeriya Biyu Kan Zargin Fashi

4 weeks ago
Harin Asibitin Gaza Ya Halaka Mutane da Dama, Ciki Har da Ƴan Jarida
Kasashen Ketare

Harin Asibitin Gaza Ya Halaka Mutane da Dama, Ciki Har da Ƴan Jarida

1 month ago
Next Post
Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (6)

Hikimar Yunƙurin Sake Farfaɗo Da Noman Filanten A Jihar Nasarawa

LABARAI MASU NASABA

Katsina Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Mahaddata Alƙur’ani – Gwamna Radda

Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina: Nasara Ko Matsala?

September 26, 2025
Kasar Sin Na Farin Cikin Ganin Kamfanoni Suna Gudanar Da Shawarwarin Kasuwanci Da Kyau Bisa Ka’idojin Kasuwa

Kasar Sin Na Farin Cikin Ganin Kamfanoni Suna Gudanar Da Shawarwarin Kasuwanci Da Kyau Bisa Ka’idojin Kasuwa

September 26, 2025
An Gano Cututtuka Uku Da Suka Ta Da Hankalin Hukumomin Lafiya A Nijeriya

An Gano Cututtuka Uku Da Suka Ta Da Hankalin Hukumomin Lafiya A Nijeriya

September 26, 2025
Kasar Sin Ta Yi Alkawarin Bayar Da Sabuwar Gudummawa Dangane Da Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya

Kasar Sin Ta Yi Alkawarin Bayar Da Sabuwar Gudummawa Dangane Da Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya

September 26, 2025
Membobin Tawagar Koli Ta Sin Sun Ziyarci Jami’ai Da Gidajen Al’umma A Yankunan Jihar Xinjiang

Membobin Tawagar Koli Ta Sin Sun Ziyarci Jami’ai Da Gidajen Al’umma A Yankunan Jihar Xinjiang

September 26, 2025
Akwai Bukatar Sin Da Amurka Su Lalubo Hanya Mafi Dacewa Ta Tafiya Tare A Sabon Zamani

Akwai Bukatar Sin Da Amurka Su Lalubo Hanya Mafi Dacewa Ta Tafiya Tare A Sabon Zamani

September 26, 2025
Mazauna Kuyello A Jihar Kaduna Na Cikin Zullumin Bayyanar ‘Yan Ta’addar Ansaru

Gwamnati Ta Kafa Kwamitin Bincike A Kan Fashewar Wani Abu A Kaduna

September 26, 2025
An Samu Manyan Sauye-Sauye Na Zamani A Jihar Xinjiang Cikin Shekaru 70

An Samu Manyan Sauye-Sauye Na Zamani A Jihar Xinjiang Cikin Shekaru 70

September 26, 2025
Trump Ya Haramta Wa Jami’an Nijeriya Masu Cin Hanci Da Rashawa Shiga Amurka

Trump Ya Haramta Wa Jami’an Nijeriya Masu Cin Hanci Da Rashawa Shiga Amurka

September 26, 2025
Gwamnatin Kogi Ta Yi HaÉ—in Gwuiwa Don Fara Fitar Da Amfanin Gona

Gwamnatin Kogi Ta Yi HaÉ—in Gwuiwa Don Fara Fitar Da Amfanin Gona

September 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.