Yau ake cika shekaru biyu da barkewar rikici tsakanin Ukraine da Rasha. Alkaluman da aka samu na nuna cewa, a cikin wadannan shekaru biyu, al’ummomin kasashen biyu sama da dubu 500 ne suka halaka, baya ga al’ummar kasar Ukraine sama da miliyan 10 da aka raba da muhallansu. Ba kawai kasashen Rasha da Ukraine rikici ya shafa ba, har ma ya haifar da hauhawar farashin makamashi da hatsi a fadin duniya, inda wasu kasashen Afirka har suka fuskanci matsalar yunwa.
Sai dai abin takaici shi ne, har yanzu babu alamar kawo karshen rikicin.
- A Kwai Bukatar Iyaye Su Tashi Tsaye Wajen Kula Da Tarbiyyar ‘Ya’yansu – Fatima Sa’ad
- Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Gwajin Fasahar Sadarwa
Duk da mummunan tasirin da rikicin ya haifar wa akasarin kasashen biyu, amma Amurka ta amfana matuka daga rikicin. Masana’antun samar da makaman soja da sauran sassa masu ruwa da tsaki na kasar sun ci kazamar riba daga rikicin, baya ga yadda kasar ta ci riba mai tsoka ta fannonin makamashi da hatsi da kasuwar hannayen jari sakamakon rikicin. Baya ga rura wutar rikicin, Amurka ta kuma yaudari Ukraine, tare da raunana Rasha da Turai da kuma fadada kungiyar tsaro ta NATO, kamar yadda Bahaushe kan ce jifar tsuntsu biyu da dutse guda. Ma iya cewa, muddin rikici ya ci gaba, to, ba za a samu kwanciyar hankali a Turai ba, abin da zai sa kasashen nahiyar su kara dogara ga Amurka, ta hakan kuma Amurka za ta kara cin gajiya da kuma kiyaye matsayinta na nuna fin karfi a duniya.
Idan mun waiwayi rikici, za mu gano cewa, ra’ayin cacar baka da nuna fin karfi shi ne ainihin abin da ya haifar da rikicin. Dalilin da ya sa Amurka ta rura wutar rikicin, shi ne kiyaye matsayinta na fin karfi a duniya, tare da cin mummunar riba. A gun taron harkokin tsaro na Munich da aka gudanar a kwanan baya, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya ce, “Ta fuskar al’amuran kasa da kasa, in dai ba a zama mai cin abinci ba, to, za a zama abinci ke nan”, furucin da ya tona mana ainihin alkiblar manufar Amurka a kan harkokin kasa da kasa, wato wadanda ke da karfi ya ke ci, yayin da wadanda ba su da karfi su ake cinye wa.
Irin yanayin da ake ciki na rashin kwanciyar hankali a duniya, ya sanya wa karin kasashe damuwar tsaronsu. Kowa na son tabbatar da tsaro, amma ta yaya hakan zai tabbata?
Domin cimma burin tabbatar da cikakken tsaro, Amurka da sauran kasashen yamma suka ware makudan kudade a bangaren soja. A gun taron ministocin tsaro na kasashen kungiyar NATO da aka kira a kwanan baya, ma’aikatar harkokin wajen Amurka da babban sakataren NATO sun sake sa kaimin kasashe mambobin NATO da su kara kasafin kudin tsaro, inda suka nemi a kalla kasashe 18 na NATO su ware kasafin kudin tsaro da yawansa ya kai kimanin kaso 2 na GDP dinsu.
Duk da kwararan matakan da kasashen suka dauka, amma yanayin tsaronsu sai kara tabarbarewa yake yi a maimakon ingantuwa, shin mene ne dalilin haka?Sabo da tsaron da Amurka da sauran kasashen yamma suke nema shi ne tsaro na kansu, maimakon tsaron Bil Adam baki daya. Sa’an nan, a yayin da suke zancen kiyaye tsaron duniya, a hakika, suna magana ne a kan kiyaye babakeren da suka kafa. Wannan ya sa, suke ta kaddamar da yake-yake da kulla kawance da wasu, da ma ta da rikici da wasu, kuma hakan ya lalata tsaron kasashen duniya na bai daya.
A hakika, ko a kasashen yamma da kasashen gabas, ko kuma a kasashe masu ci gaba da kuma kasashe masu tasowa, burin al’ummar kasa da kasa daya ne, wato a tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasashensu. Abin da kawai ya bambanta shi ne wane irin tsaro ne muke so?
Game da wannan tambaya, kasar Sin ta ba da amsarta bisa shawarar kiyaye tsaro na duniya da ta gabatar, wato Global Security Initiative a Turance, inda ta shawarci kasa da kasa da su yi kokarin tabbatar da tsaronsu na bai daya. A gun taron harkokin tsaro na Munich a wannan karo, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gabatar da jawabi, inda ya yi nuni da cewa, kamata ya yi kasa da kasa su yi kokarin neman cin nasara tare, kuma su hada kai da juna. Ya jaddada cewa, kasar Sin na bin shawarar kiyaye tsaro na duniya, kuma tana kokarin neman cimma daidaito tsakanin kasa da kasa game da batun tsagaita bude wuta a rikicin Ukraine da Rasha, tare da share fagen yin shawarwarin shimfida zaman lafiya.
A ganin kasar Sin, kasashen duniya makomarsu daya ce, kuma babu kasar da za ta iya tsira daga tashe-tashen hankula da ake fuskanta a sassan duniya.
Domin fita daga mawuyacin halin tsaro da suke ciki, ya kamata kasashen yamma su gyara tunaninsu na cin nasara daga faduwar wani bangare. Illa dai kasashen duniya su hada hannu wajen kiyaye tsaronsu na bai daya, daga karshe za a kai ga daidaita matsalar Ukraine daga tushe, da ma tabbatar da dauwamammen zaman lafiya da tsaro a duniya.