A yau Litinin, aka kammala taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin a babban dakin taron al’umma dake birnin Beijing. Xi Jinping, wanda aka zaba a matsayin shugaban kasar Sin a karo na 3, ya gabatar da jawabi yayin rufe taron.
Me jawabin nasa ya kunsa?
Sanya jama’a gaba da komai
Xi Jinping ya ce amincewar da jama’a suka yi da shi, ita ce ke ba shi kwarin gwiwar ci gaba da yin aiki, kuma babban nauyi ne da ya rataya a wuyansa.
Bayan kasancewarsa shugaban kasar Sin, ya taba cewa, “Tun da jama’a ne suka ba ni wannan matsayi, za su kasance kan gaba a cikin zuciyata a ko da yaushe.”
Aiwatar da aikin farfado da kasa yadda ya kamata
A jawabinsa, Xi ya ce ya nazarci manufar JKS ta jagorantar Sinawa a gwagwarmayar neman makoma mai haske a kasar. Ya ce bayan shekaru 100 ana gwagwarmaya, farfado da al’ummar Sinawa ya kai wata gaba a tarihi, wadda ba za a iya mayar da ita baya ba.
Ya kuma yi alkawarin samar da nasarorin da za su dace da zamani, da tarihi, da bukatun jama’a.
Inganta gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil adama
Cikin jawabinsa, Xi ya sake yin bayani kan tunaninsa na inganta gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil adama. Ya ce, ci gaban kasar Sin zai yi wa duniya amfani, kuma ba za a iya kebe ci gaban kasar daga sauran sassan duniya ba. Ya ce Sin za ta shiga a dama da ita wajen aiwatar da sauye-sauye a tsarin jagorantar duniya da inganta aiwatar da shawarwarin raya duniya da na tabbatar da tsaro a duniya, tare da kara kwanciyar hankali da kuzari ga zaman lafiya da ci gaban duniyar. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp