Enzo Maresca ya amince da rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea don zama sabon kocinta, wanda zai gaji Mauricio Pochettino.
Ana sa ran za a sanar da yarjejeniyar a hukumance kafin ƙarshen mako. Maresca, wanda ya jagoranci Leicester City komawa gasar Premier ta hanyar lashe gasar Championship, an zabe shi ne saboda zurfin iliminsa na tawagar Chelsea da kuma iya daidaitawa ƴan wasa da falsafar wasan ƙungiyar.
- Toni Kroos Zai Yi Ritaya Daga Kwallon Kafa Bayan Gasar Euro
- Lookman Ya Zura Kwallo Uku Rigis Yayin Da Atalanta Ta Lashe Kofin Europa LeagueÂ
Darektocin wasanni na Chelsea, Paul Winstanley da Laurence Stewart, sun tattauna tare da Maresca bayan sun sami izini daga Leicester City. Rahotanni sun ce yarjejeniyar sakin dan ƙasar Italiyan daga Leicester ya kai fam miliyan 8 zuwa fam miliyan 10.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp