Wakilin din din din na kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva, da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland Chen Xu, ya mika wa babban darektan hukumar Kwadago ta Kasa da Kasa wato ILO a takaice, takardu guda biyu, game da amincewar da kasar Sin ta yi da Yarjejeniyar Aikin Tilas ta shekarar 1930 mai lamba 29, da ta Kawar da Yarjejeniyar Aikin Tilas ta shekarar 1957 mai lamba 105.
Yarjejeniya ta 29 da ta 105, na cikin muhimman yarjejeniyoyi 10 na ILO, kuma su ne dokokin kasa da kasa mafi mahimmancin a fagen kawar da aikin tilas.
A watan Afrilun bana, aka yanke shawarar amincewa da manyan yarjejeniyoyin biyu, a yayin taro karo na 34, na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 13.
A ko da yaushe, gwamnatin kasar Sin tana adawa da aikin tilas, kuma amincewar ta da wadannan yarjejeniyoyin guda biyu da kanta, ya kara nuna tsayuwar daka da gwamnatin kasar Sin ke yi, game da kare hakki da muradun ma’aikata, da adawar ta, da ma yaki da ayyukan tilas. (Mai fassara: Bilkisu Xin)