Ministan Birnin Tarayya Abuja, Malam Muhammad Bello, ya yi alkawarin tallafa wa harkokin gidauniyar tunawa da Ahmadu Bello a cikin Abuja da kewaye.
Ministan ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin da kwamitin gudanarwar gidauniyar ta kai masa ziyara a ofishinsa a Abuja a ranar Alhamis.
Ministan ya ce, Marigayi Sir Ahmadu Bello, ya yi tasiri a rayuwarsa a lokacin yana dalibi, haka kuma ya yi tasiri a rayuwar ‘yan Nijeriya da dama.
Ya kuma nuna jin dadinsa ga ayyukan jin kai da gidauniyar take yi a Abuja musamman a lokaci da aka fuskanci annobar Korona kwanakin baya.
Daga nan ne ‘yan kwamitin suka karrama ministan da lambar girmamawa ta gidauniyar, an yi ziyara ne a karashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Neja Dakta Muazu Aliyu.
Dakta Mu’azu Aliyu, ya yaba da yadda ministan yake gudanar da ayyukansa a Abuja, ya kuma gode masa a kan irin tallafin da yake bai wa gidauniyar.
Cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau da shugaban gudauniyar, Abubakar Umar.