Mamban majalisar gudanarwa ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, ya gana da takwaransa na kasar Equatorial Guinea Simeon Oyono Esono Angue jiya Alhamis a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Yayin ganawar, Qin ya yi alkawarin baiwa kasar Equatorial Guinea goyon baya a kai a kai, wajen gudanar da bincike kan hanyar samun ci gaba da ta dace da yanayin kasar, da kiyaye ikon mallakar kasa, da adawa da tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidanta.
Ya kara da cewa, ana karfafawa kamfanonin kasar Sin gwiwa, da su zuba jari a kasar Equatorial Guinea, kuma kasuwar kasar Sin na maraba da karin kayayyakin da ake samu daga Equatorial Guinea.
Qin ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa Afirka, wajen samun farfadowar tattalin arziki da ci gaba mai dorewa, da sa kaimi ga gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma a sabon zamani.
A nasa jawabin ministan harkokin wajen Equatorial Guinea ya ce, kasar Sin kawa ce ta gaske, ’yar uwa ta gari, kuma abokiyar huldar Equatorial Guinea da Afirka, kuma babu abin da zai hana su zurfafa zumunci da hadin gwiwa da kasar Sin. (Ibrahim)