Ministan lafiya na kasar Kamaru, Manaouda Malachie ya bayyana jiya Talata 22 ga wata a Yaounde cewa, hadin-gwiwar Kamaru da Sin a bangaren kiwon lafiya ta haifar da babban alfanu ga jama’ar Kamaru, kana alama ce dake shaida dangantakar kut da kut gami da dadadden zumunci tsakanin jama’ar kasashen biyu.
A wajen bikin cika shekaru 50 da kaddamar da hadin-gwiwar Sin da Kamaru ta fuskar kiwon lafiya wanda aka yi a jiya Talata a birnin Yaounde, minista Malachie ya gabatar da jawabi yana mai cewa, hadin-gwiwar kasashen biyu ta fuskar kiwon lafiya ta shaida cewa, kwalliya za ta iya biyan kudin sabulu, idan aka raya hulda mai aminci, da sahihanci kuma bisa muradu iri daya tsakanin kasa da kasa.
- Gwamna Sule Ya Ƙara Musanta Zargin Kare Ƴan Ta’adda A Nasarawa
- Har Yanzu Yaƙi Da Ta’addanci Ne Babban Muradin Gwamnatina — Tinubu
Babbar jami’a a ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Kamaru, Chen Ya’ou ta bayyana nasarorin da tawagar ma’aikatan lafiyar kasar Sin ta samu a kasar ta Kamaru cikin shekaru 50 da suka gabata.
Rahotannin sun ruwaito cewa, tun daga shekara ta 1975, zuwa yanzu, Sin ta tura tawagogin ma’aikatan lafiya guda 24 zuwa Kamaru, dake kunshe da mutane 786 gaba daya, wadanda suka samar da hidimomin jinya tare da samun babban yabo daga jama’ar kasar. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp