Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov jiya Lahadi a birnin Beijing, inda ya yi masa maraba da zuwa taron ministocin kasashe membobin dandalin hadin gwiwar Shanghai ko SCO.
Wan Yi, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da Rasha, da sauran kasashe mambobin SCO wajen gudanar da taron na birnin Tianjin, da daga matsayin dandalin na SCO zuwa sabon matsayi.
- Gwamna Abba Ya Yi Alhinin Rasuwar Muhammadu Buhari
- Za A Yi Taron Shugabannin Matasa Na Farko Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka A Nanjing
Ya ce a bana ake bikin cika shekaru 80, da cimma nasarar yakin da Sinawa suka gwabza don nuna adawa da mamayar dakarun Japan, kuma ya dace sassan biyu su gudanar da ayyuka na tunawa da cika shekaru 80, da cimma nasarar yakin duniya na biyu da kiyaye ainihin tarihin yakin.
A nasa bangare kuwa, mista Lavrov bayyana aniyar kasarsa ya yi ta yin aiki tukuru tare da Sin, wajen zurfafa hadin gwiwa a mabanbantan fannoni, karkashin managarcin jagorancin shugabannin kasashen biyu, da ingiza sabbin nasarori a alakar sassan biyu.
Ya ce Rasha za ta ci gaba da mara baya ga Sin bisa jagorancin karba-karba na dandalin SCO, da inganta tattaunawa, da hadin gwiwa karkashin tsare-tsaren ayyukan SCO da sauransu, tare da tabbatar da kammala taron SCO na birnin Tianjin cikin nasara. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp