Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya yi kira da a yi kokarin sa kaimi ga bunkasuwar dunkulewar duniya baki daya, da karfafa hadin gwiwar bangarori daban-daban a yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 da ake yi a New Delhin kasar Indiya
Yayin da yake gabatar da jawabin karfafa hadin gwiwar bangarori daban-daban da inganta ci gaban duniya a yayin taron Alhamis din nan, Qin ya bukaci manyan kasashe masu karfin tattalin arziki, da su dauki nauyin yin aiki tare domin ci gaban duniya da samun wadata. (Ibrahim Yaya)