Jiya Lahadi 1 ga wata ministan harkokin wajen kasar Sin kuma jakadan kasar dake kasar Amurka Qin Gang ya tattauna da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ta wayar tarho, inda Qin Gang ya yi ban kwana da Blinken, tare kuma da waiwayi ganawar da suka yi, yayin da yake kasancewa jakadan dake Amurka. Kana yana fatan zai ci gaba da kiyaye huldar aiki mai kyau dake tsakaninsu, ta yadda za a ingiza kyautatuwa da ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Amurka.
Haka zalika sassan biyu sun isar da gaisuwar sabuwar shekara ga junansu. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp