Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalin su bayan dakatar da gidan rediyon Badeggi FM da ke Minna da Gwamnatin Jihar Neja ta yi.
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, shi ne ya bayar da umarnin rufe tashar , kamar yadda rahotanni suka nuna, a yayin wani taron faɗaɗa na tsangayar jam’iyyar APC da aka gudanar a Minna a ranar 1 ga Agusta.
- Sanata Buba Ya ƙaryata Jita-jitar Cewa Majalisa Ta Amince da ƙirƙiro Sabbin Jihohi 12
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji
Rahotanni sun ce gwamnan ya zargi rediyon da rashin bin ƙa’idar aiki a cikin shirye-shiryen sa da kuma tayar da zaune tsaye kan gwamnati.
Minista Idris ya bayyana damuwa da irin martanin da al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai suka nuna dangane da lamarin. Amma ya jaddada cewa hukumar da ke da hurumin dakatar da lasisin gidajen rediyo da talabijin ita ce Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), kamar yadda doka ta tanada.
Sanarwar da Gwamnatin Tarayya ta bayar kan lamarin ta ce: “Saboda haka, ministan yana maraba da matakin da Gwamnatin Jihar Neja ta ɗauka na kai koken da ta ke da shi kan zargin rashin ɗabi’a da Badeggi FM ta yi a hukumance zuwa ga NBC domin a warware batun.”
Idris ya roƙi dukkan ɓangarori da su kwantar da hankalin su, yana mai tabbatar da cewa NBC tana da tsarin da ya dace na warware irin waɗannan matsaloli cikin gaskiya da adalci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp