Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Garba Yakubu, da ɗaukacin iyalansa bisa rasuwar matarsa, Hajiya Zainab.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, ministan ya ce, “Ina miƙa saƙon ta’aziyyata ga Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Mai Girma Alhaji Garba Yakubu, da ɗaukacin iyalansa bisa rasuwar mai ɗakinsa, Hajiya Zainab.
- An Aike Ɗan Shekara 67 Gidan Yari Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Mata 2 Fyaɗe Yana Ba Su ₦500 A Bauchi
- Muna Jaddada Kiran A Tsame Masarautunmu Daga Rikicin Siyasa
“Kalamai ba za su iya bayyana baƙin ciki da juyayin da mu ke yi wa Mataimakin Gwamna a wannan lokaci mai matuƙar wahala ba.
“Marigayiya Zainab fitacciyar mace ce wadda kyautatawarta da sadaukarwarta su ka taɓa rayuwar mutane da yawa.
“Gudunmawar da ta bayar a Jihar Neja ya bar wa waɗanda su ka yi sa’a da saninta tarihin da ba zai kankaru ba.
“Haƙiƙa, rasuwarta babban rashi ne ba ga Jihar Neja da mata ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
“A wannan lokaci na makoki, tunanin mu da addu’o’in mu su na tare da Mataimakin Gwamna. Mu na tare da shi, mu na ba da goyon baya da ƙarfin mu yayin da ya ke ji da wannan babban rashi.
“Allah ya jiƙan ta ya kuma bai wa Mataimakin Gwamna da sauran iyalin sa gaba ɗaya ƙwarin gwiwar jure wannan rashi mara misaltuwa.”