Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya tsohon Shugaban Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, GCFR, murnar cikar sa shekaru 84 a duniya.
A cikin wata sanarwa, Idris ya bayyana tsohon shugaban a matsayin “ɗan siyasa na gaskiya wanda rayuwar sa da hidimar sa suka kasance a rubuce kundin tarihin siyasar Nijeriya.”
- Filato Ta Tsakiya Ta Amince Da Tazarcen Mutfwang A 2027
- Mutane 62 Sun Kuɓuta A Wani Hari Da NAF Ta Kai Wa ‘Yan Bindiga A Katsina
Ya ce Babangida ya ci gaba da kasancewa murya ta hikima, daidaito, da jagora a tafiyar Nijeriya ta neman zaman lafiya, haɗin kai, da cigaba mai ɗorewa.
Ya ƙara da cewa: “Yayin da ya kai wannan muhimmin zango, muna murnar ba wai yawan shekarun sa kawai ba ne, har ma da gagarumar gudunmawar da ya bayar ga cigaban Nijeriya ta zamani, musamman ta hanyar jagorancin sauye-sauyen siyasa da tattalin arziki. Gado na hidima, jarumtaka, da hangen nesa da ya bari na ci gaba da zaburar da shugabanni da ’yan ƙasa baki ɗaya.”
Idris ya kuma bayyana cewa “a yayin da ya kai shekara 84, Janar Babangida ya kasance babbar rijiya ta ilimi da ƙwarewa, yana ci gaba da zaburar da al’ummomi daban-daban ta hanyar tsantsar tunani da zurfin fahimta.”
Ministan ya yi addu’ar cewa Allah ya ƙara wa Babangida shekaru masu albarka cikin ƙoshin lafiya, kuzari, da cikar buri, inda ya ce: “Allah ya sanya wannan sabon babi na rayuwar sa ya kasance cikin zaman lafiya, farin ciki, da ƙaunar ƙasa mai godiya wadda take mutunta shi matuƙa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp