A ranar Litinin din nan Majalisar Dattijai ta kammala aikin tantance Ministocin 48 da shugaba Tinubu ya aike mata a makon da ya gabata, sai dai uku daga cikin ministocin ba su shellake ba.
Majalisar ta kwashe kimanin mako guda tana tantance ministocin 48, inda ta fara ranar Litinin, 31, ga watan Yuli, 2023 zuwa Litinin, 7, ga watan Augusta 2023.
- Majalisa Ta Tantance Mairiga Wacce Ta Maye Gurbin Shetty A Matsayin Minista Daga Kano
- Tinubu Ya Janye Sunan Maryam Shetty Cikin Ministoci
Sai dai majalisar ba ta tabbatar da uku daga cikin wadanda aka aike mata ba saboda rahoton tantacewa daga DSS. Mutum ukun sun hada da Nasir El-Rufai daga Kaduna, Stella Okotete daga jihar Delta sai kuma Abubakar Sani Danladi daga jihar Taraba.
Majalisar ta tantance ministoci 45 cikin 48 da suka hada da:
1. Akwa Ibom: Ekperikpe Ekpo
2. Bayelsa: Heineken Lolokpobri
3. Cross River: Betta Edu
4 Cross River: John Owan Enoh
5. Delta: Stella Okotete ❌
6 . Delta: Festus Keyamo
7. Edo: Abubakar Momoh
8. Rivers: Nyesom Wike
9. Adamawa: Tahir Mamman
10. Bauchi: Yusuf Maitama Tuggar
11. Bauchi: Ali Pate
12. Borno: Abubakar Kyari
13. Gombe: Alkali Ahmed Saidu
14. Taraba: Uba Maigari Ahmadu
15. Yobe: Ibrahim Geidam
16. Taraba: Sani A Danladi ❌
17. Jigawa: Mohamed Badaru
18. Kaduna: Nasir El-Rufai ❌
19. Kano: Mariya Mahmoud Bunkure
20. Kano: Abdullahi Tijjani Gwarzo
21. Katsina: Ahmad Dangiwa
22. Katsina: Hannatu Musawa
23. Kebbi: Yusuf Tanko Sununu
24. Kebbi: Atiku Bagudu
25. Sokoto: Bello M Goronyo
26. Zamfara: Bello Matawwalle
27. Abia: Nkiru Onyejiocha
28. Anambra: Uju Ohaneye
29. Ebonyi: David Umahi
30. Enugu: Uche Nnaji
31. Imo: Doris Uzoka
32. Ekiti: Dele Alake
33. Lagos: Tunji Alausa
34. Lagos: Lola Ade John
35. Ogun: Ishak Salako
36. Ogun: Bosun Tijani
37. Ogun: Olawale Edun
38. Ondo: Olubunmi Tunji-Ojo
39. Osun: Adegboyega Oyetola
40. Oyo: Adebayo Adelabu
41. Benue: Joseph Utsev
42. FCT: Zaphaniah Bitrus Jisalo
43. Kogi: Shaibu Abubakar Audu
44. Kwara: Lateef Fagbemi, SAN
45. Nasarawa: Imaan Sulaiman-Ibrahim
46. Niger: Mohammed Idris
47. Niger: Aliyu Sabi Abdullahi
48. Plateau: Simon Bako Lalong