A yayin da ake ci gaba da sauye-sauyen tsare-tsare a Nijeriya, alamu sun nuna cewa nan ba da jimawa ba Shugaba kasa Bola Tinubu zai yi wa majalisar ministocinsa garambawul domin kawar da ministocin da ba su yi aiki ba.
Wata majiya mai tushe wacce ta nemi a sakaya sunanta a fadar shugaban kasa ta bayyana hakan a kwanan nan.
- MOF: Kasar Sin A Shirye Take Ta Zurfafa Hadin Gwiwa Da Dukkan Bangarorin GDI
- Rodri Ba Zai Sake Buga Kwallo A Wannan Kakar Ba Sakamakon Rauni
A cewar majiyar, shugaban kasar ya damu matuka da yadda akasarin ‘yan ministocinsa ba su tallafa wa gwamnatinsa wajen cike burin ajandarsa ta sabunta fata, sannan akwai matsananciyar matsin lamba na yin garambawul ga majalisar ministocinsa.
Majiyar ta ce za a iya sauke wasu daga cikin ministocin, yayin da wasu kuma za a iya sauya musu wuraren aikinsu na asali, wasu kuma a bar su a inda suke aiki domin samun kyakkyawan shugabanci.
Majiyar ta bayyana cewa ba yi wa majalisar ministocin garambawul tun da farko ba saboda tunuanin siyasar zaben 2027.
Majiyar ta ci gaba da cewa, “Shugaban kasa ya damu matuka saboda yawancin ‘yan majalisar ministocinsa ba su da wani shiri na tafiyar da ajandarsa ta sabunta fata. An dai sha matsin lamba a kan ya yi wa majalisar ministoci garambawul, amma saboda wasu dalilai na siyasa ya ki yin hakan. Yawancin ministocin manyan masu ruwa da tsaki ne a siyasance wadanda ba a iya yin watsi da tasirinsu ba. Tasirin siyasar ne zai taimaka wa shugaban kasa a 2027 domin ya aiwatar da wa’adinsa na biyu. Don haka, gwargwadon yadda shugaban kasa zai so ya nada masu basira domin tafiyar da manufofinsa wajen cimma burinsa, akwai kuma bukatar yin wasu dubaru na siyasa. Saboda haka, kwazon ministocin ba shi kadai shugaban kasa yake la’akari da shi ba wajen yanke shawara.”
A kan ministocin da ake ganin za a tsige idan shugaban kasa ya yanke shawarar yin garambawul a majalisar ministocinsa, wata majiya ta ce, “Ba zai iya gaya muku adadin wadanda za a cire ba. Amma akwai yuwuwar canza wa wasu wuraren ayyuka.
“Duk da haka, akwai wasu daga cikinsu wadanda lamarin ba zai shafan su ba. Wasu kwazansu ne zai cece su, yayin da wasu kuma za su tsira ne sakamakon tasirinsu a siyasa da dangantakarsu da shugaban kasa.
“Wadanda ake ganin za su sha sun hada da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike; ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate; ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo, ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo; ministan kudi, Wale Edun; ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Atiku Bagudu da ministan ayyuka, Dabe Umahi.