Dan Wasan kasar Masar da Liverpool, Mohamed Salah ya sabunta kwantaraginsa da kungiyar bayan shafe tsawon lokaci ana tunanin zai bar kungiyar.
Salah ya sabunta kwantaraginsa ne a ranar Juma’a, lokacin da ya ke hutu kafin koma daukar horo a kungiyar nan da mako biyu masu zuwa.
- Kotun Daukaka Kara Ta Daure Sanata Nwaoboshi Shekara 7 Bisa Laifin Almundahana
- Dan Majalisar Edo Jude Ise-Idehen, Ya Rasu
Salah ya sake sanya wa Liverpool kwantaragin shekaru uku a kungiyar, wato zuwa karshen 2025.
Kafin sabunta kwantaragin nasa, an yu zargin zai bar Liverpool, inda aka dinga hasashen Real Madrid, Barcelona da PSG na son daukarsa.
Dan wasan ya dauki lokaci yana tattaunawa da Liverpool kan sabunta kwantaragin wanda ya bukaci karin albashi da alawus.
A satin da ya wuce ne Liverpool ta yi bankwana da Sadio Mane zuwa kungiyar Bayern Munich da ke kasar Jamus.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp