Mohamed Salah, ɗan wasan gaba na Liverpool daga ƙasar Masar, ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan Firimiyar Ingila a bana.
- Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba
- Budurwa ƴar shekara 15 Ta Jefar Da Jariri A Sansanin Ƴan Gudun Hijira A Borno
Wannan ne karo na biyu da ya samu wannan gagarumar nasara, bayan wanda ya samu a shekarar 2017.
An ba shi wannan kyautar ne bayan haɗa ƙuri’u daga jama’a da kuma kwamitin masana ƙwallon ƙafa.
Salah ya doke ‘yan wasan da suka haɗa da Virgil van Dijk da Ryan Gravenberch daga Liverpool, Morgan Gibbs-White da Declan Rice daga Arsenal, Alexander Isak daga Newcastle, Bryan Mbeumo daga Brentford da Chris Wood daga Nottingham Forest.
Wannan shi ne karo na farko tun 2018 da wani ɗan wasa da ba na Manchester City ba ya lashe wannan kyauta.
Kafin wasan ƙarshe na bana da za su kara da Crystal Palace a ranar Lahadi, Salah ya riga ya ci ƙwallaye 28 a Firimiyar bana kuma ya taimaka a ci wasu 18.
Kusan taimako biyu kawai suka rage masa ya kai tarihin taimako 20 da Thierry Henry da Kevin de Bruyne suka kafa.
A wannan kakar, Salah ya zama ɗan wasan da ba na Ingila ba da ya fi zura ƙwallaye kwallaye a tarihin Firimiyar Ingila, inda ya zarce ƙwallaye 184 da Sergio Aguero ya ci.
Haka kuma ya sabunta kwantiraginsa da Liverpool har zuwa shekarar 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp