An shafe shekaru masu yawa, tun ma kafin samun ‘yancin Nijeriya, fitattun ‘yan jarida da mawallafa su na taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasar Æ™asar nan. Sun tsunduma siyasa ne baya ga ayyukan sadaukarwar da su ka riÆ™a yi wa jama’a a gidajen jaridu. A duniya ma masu kafafen yaÉ—a labarai sun zama mashahuran shugabanni da manyan ‘yan siyasa.
Kafin ma a samu ‘yanci kafafen yaÉ—a labarai sun kasance masu bayar da gagarumar gudunmawar neman ‘yanci. Kuma masu kafafen yaÉ—a labaran nan da ‘yan jarida sun yi rawar gani sosai a manyan muÆ™aman siyasa. Kafin samun ‘yanci an samu bayyanar manyan masu damawa a harkokin jarida sun zama mashahuran ‘yan siyasa, wato Sa Herbert Macaulay da Dakta Nnamdi Azikiwe, wanda shi ne ya zama Shugaban Ƙasa na farko a ranar da Nijeriya ta samu ‘yanci, wato 1 ga Oktoba, 1960.
Fitattun ‘yan jarida da masu gidajen jaridu sun ci gaba da kutsawa cikin harkokin siyasa, tun daga wancan lokacin har zuwa yau, inda a Jamhuriya ta Biyu aka samu biyu daga cikin su sun yi nasarar zama gwamna: Lateef Jakande ya zama Gwamnan Jihar Legas, Segun Osoba kuma ya zama na Jihar Ogun.
WaÉ—ansun su kuma da dama sun riÆ™e muÆ™amai daban-daban, tun daga ‘yan majalisa, ciyamomi da kansiloli, ko kuma sun riÆ™e shugabancin wasu hukumomi da cibiyoyi.
A cikin Oktoba 2019, mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya yanke shawarar shiga wancan daji na siyasa da manyan ‘yan jarida da mawallafa su ka keta. Da ya shiga kuwa, ya fito gadan-gadan neman muÆ™amin siyasa. Tun daga lokacin kuwa tafiya mai nisan zangon watanni 31 ana tuntuÉ“ar jama’a, ganawa, kamun-Æ™afa da tattauna yadda za a kai ga cimma nasara.
Lokacin da Malagi ya fito, wasu mutane sun riÆ™a cewa ya dai fito ne don ya tayar da Æ™ura kawai. Wasu ma cewa su ke yi wasa ya ke yi. Akwai kuma masu yi masa kallon mutumin da ya yi samun kuÉ—in da ake cewa ‘dare É—aya Allah kan yi Bature’, wanda ya rasa yadda zai kashe kuÉ—in sa, wai shi ya sa ya shiga siyasa, kawai don ya yi É“arusa. Akwai wasu da su ka riÆ™a yi masa kallon sabon-yanka-rake ne a siyasa, wanda a ganin su bai isa ya yi gasa da tsofaffin ‘yan alewar siyasa ba.
Dukkan waɗanda su ka riƙa tofa albarkacin bakin su dangane da shigar Malagi siyasa sun yi tsammanin da ya fara, za a neme shi a rasa, wato zai yi tashin kumfar gishirin Andurus. Sun yi tsammanin ya shiga ne kawai don neman suna.
Da ma haka aka riƙa yi masa irin wannan mummunar fassara lokacin da ya fara wallafa jaridar Blueprint. Saboda ya shiga harkar da ƙarfin sa, har ya girgiza waɗanda su ka fara yi masa kallon raini a lokacin. To irin haka lamarin ya maimaita kan sa lokacin da ya shiga siyasa, inda manyan masu ruwa da tsaki da masu ganin sai irin su wane da wane ke iya yin gwamna a Jihar Neja su ka riƙa yi masa kallon sabon-shiga.
Malagi ya shafe watanni 30 ana gwagwagwa da shi, inda ya jajirce, ya nuna cewa shi fa ya kawo ƙarfi, don haka ya fi wane ya girme ni.
Daga lokacin da ya fara zuwa lokacin da ya fara shiga cikin zukatan jama’ar sa, Alhaji Mohammed Idris ya shimfiÉ—a hajar siyasar sa a farfajiyar Jihar Neja, inda ya riÆ™a shelar siyasar da babu tashe-tashen hankula, a gefe É—aya kuma ya na kutsawa garuruwa da lunguna ya na jaddada kamfen a bisa batutuwan da su ka shafi cigaban jiha da al’ummar ta baki É—aya.
Yayin da sauran ‘yan siyasa su ka mayar da hankali su na yarfe da bankaura ta hanyar amfani da soshiyal midiya, su ka riÆ™a raba kawunan jama’a, shi kuwa ci gaba ya yi da yi wa jama’a albishir da muhimmancin haÉ—in kai domin a gina Æ™asaitacciyar Jihar Neja.
Cikin wannan lokacin ya gana da masu ruwa da tsaki na kowace shiyya a jihar. Dalilin haka abin koyi hatta ga su kan su abokan adawar siyasa, waÉ—anda kafin shigar Malagi siyasa ba su iya zama inuwa É—aya.
Malagi ya riÆ™a kai wa dattawan jiha ziyara, su da sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da jagororin jama’ar yankunan karkara. Kuma ya jawo matasa, dattawa da maza da mata. Sannan ya riÆ™a yin la’akari sosai da masu ruwa da tsakin APC mai mulki a jihar.
Ya yi amfani da kuÉ—in sa da lokacin sa da tsarin tafiyar sa har ya yi nasarar ratsa zukatan ‘yan jam’iyyar APC reshen Jihar Neja. Ya taka rawa sosai wajen bai wa jam’iyyar gudunmawa. Akwai lokacin da ya bayar da gudunmawar motoci 31 da naira miliyan 43.
Lokacin da ya ke yankar tikitin takarar gwamna, Malagi, wanda a yanzu shi ne Kakaaki Nupe, ya nanata babban dalilin sa na neman tsayawa takarar gwamna. Ya ce: “Niyya ta domin ganin na ciyar da Jihar Neja gaba ta bunÆ™asa a fili ta ke. Idan na zama gwamna zan yi aiki tuÆ™uru, tun daga sa’ar farkon shiga ta ofis domin in zaÆ™ulo zarata kuma Æ™wararru daga cikin maza da mata, matasa, masu ilmi da marasa ilmi, manoma, masu sana’o’in hannu, ‘yan tireda, kai da kowa da kowa, domin su bayar da gudunmawar da za su iya bayarwa.”
Tun daga lokacin da ya fara tuntuÉ“ar jama’a, bai taÉ“a yarda zuciya ta É—ebe shi ya yi abin da ya saÉ“a wa kyawawan halaye da É—abi’un sa ba. Yayin da wasu ‘yan siyasar jihar su ka rungumi ‘yan daba, siyasar Æ™iyayya, ramuwar gayya da É“ata sunan abokin hamayya, shi kuwa sai ya mai da hankali wajen kamfen É—in rashin tayar da hankula, haÉ—in kai da zaman lafiya. Sai da ya tuntuÉ“i dukkan ‘yan takarar gwamna a Æ™arÆ™ashin APC na Jihar Neja. Kuma irin wannan albishir ya riÆ™a yaÉ—awa a lokacin ganawar sa da Æ™ananan hukumomi da mazaÉ“un ‘yan Majalisar Tarayya na jiha.
A rangadin da ya yi tun daga Lapai zuwa Agaie, zuwa Bida, Kutigi da Borgu, har Kontagora da Minna, ya riÆ™a ganawa da sarakunan gargajiya, shugabannin karkara da ‘yan siyasa, bai taÉ“a yin wani furuci da zai harzuÆ™a wasu ko ya yi kalamin da zai rura wutar jituwa ba.
Kakaaki Nupe ya yi takara kuma an fafata da shi sosai. Lokacin da sakamakon zaÉ“en bai yi masa daÉ—i ba, tangarÉ—ar rashin gudanar da zaÉ“en kamar yadda Æ™a’ida ta gindiya bai hana shi fara taya murna ga wanda aka bayyana da yin nasara ba. Ko a bayan zaÉ“en fidda-gwanin an riÆ™a yi wa Malagi kallon da bai kamata ba a cikin jiga-jigan APC na jihar, amma ya dake tare da kai zuciya nesa.
Rashin nasarar da ya yi bai hana shi cika wa Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) reshen Jihar Neja alÆ™awarin motar da ya yi masu ba. A ziyarar godiya da su ka kai masa, ya ce shi ba shi da abokin gaba a ciki ko a wajen harkar siyasa.
Duk da yake an yi zaÉ“en fid da gwanin APC wanda aka yi hasashen shi ne zai yi nasara, amma hakan bai yiwu ba, a fili dai an bayyana cewa bai yi nasara a zaÉ“en ba, to amma kuma ai ya samu galabar riÆ™e alaÆ™ar siyasa. Ya shiga tare da yin tasiri sosai a zukatan miliyoyin ‘yan Jihar Neja da sauran ‘yan Nijeriya masu cike da sanin cewa babban burin Malagi shi ne ya bunÆ™asa Jihar Neja.
Wata uku bayan zaÉ“en fid da gwanin, yanzu shi ne ya kasance abin kwatance a duk faÉ—in jihar. Kowa ya na nuna so da shauÆ™in yin kusanci da shi. Ana yi masa kallon sani sabon tauraron siyasar Jihar Neja, wanda duk sauran jam’iyyu ke shauÆ™in neman ya canja sheÆ™a ya koma cikin su, su tsayar da shi takarar gwamna kawai.
Mohammed Idris, É—an shekara 56 a duniya, mawallafin jarida ne kuma Æ™warraren masanin iya hulÉ—a da jama’a. Yanzu ya zama wata rana da ta fito a siyasar Jihar Neja, wadda tafin hannu ba zai iya rufe ta ba. Ko ma dai me za a sake nanatawa dangane da sakamakon zaÉ“en fid da gwani da yadda aka gudanar da zaÉ“en, za a iya cewa an É—auki Æ™waƙƙwaran darasi don gaba.