Wani hatsarin mota ya jikkata mutane 22 da ke tattakin bikin Kirsimeti a Gombe, babban birnin Jihar Gombe.
Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, lokacin da mabiya addinin Kirista ke gudanar da tattaki a cikin garin, kamar yadda suka saba duk shekara.
- Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Goge Munanan Abubuwan Da Suka Shafi Kasar Sin A Cikin Kudurin Manufofin Tsaro Na Shekara-shekara
- Kirismeti: NDLEA Ta Cafke Mutane 34 A Wuraren Sayar Da Miyagun Kwayoyi A Kano
Kakakin ’yansandan Jihar Gombe, ASP Buhari Abdullahi, ya ce wata mota ƙirar Sharon da aka loda wa kayan hatsi ta afka cikin masu tattakin daga baya, ta buge mutane da dama.
“Mutane da dama sun ji raunuka, wasu ma har da karaya, kuma an garzaya da su zuwa asibiti don samun kulawa,” in ji ASP Abdullahi.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun ceci direban motar daga hannun mutane da suka yi yunkurin dukansa, wanda hakan ya kusa haddasa tashin hankali.
Duk da wannan hatsari, masu tattakin sun kammala shirin da suka tsara na bikin Kirsimeti cikin nasara.
A ranar Laraba, mabiya addinin Kirista a faɗin duniya suka yi murnar zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu.
Bikin Kirsimeti ya gudana cikin lumana a yawancin wurare a Nijeriya, ba tare da rahoton wani tashin hankali ba.
Sai dai gabanin bikin, an samu rahoton turmutsitsin rabon abinci a Abuja da jihohin Anambra da Oyo, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da yawa.
A Okija, Jihar Anambra, mutum 22 sun rasa rayukansu; a Abuja, mutum 10 ne suka mutu, yayin da a garin Ibadan, Jihar Oyo, yara 35 suka mutu a turmutsitsin.