Matsalar bai wa yara rashin kulawa daga bangaren iyaye, inda za ka ga wasu iyayen basu damu da jan ‘ya’yan su a jiki ba, har su san damuwarsu, irin wannan yana kawo matsalar da a Turanci ake kira ‘depression’, a bisa nazarin masana halayyar dan Adam. Kuma hakan har wa yau ya zo daidai da fahimtar wata malamar makaranta Aishatu Suleiman Abubakar da ke Jos da marubuciya Rahama Sabo Usman da ke Kano, wadanda ke ganin lalacewar tarbiyyar iyaye ne ke jawo wa, saboda rashin jan yaransu a jiki da ba su fuskar da za su amayar da damuwarsu ko neman shawara.
Sannan kuma ana iya samun wannan matsalar a tsakanin ma’aurata da suke samun matsala ta fahimtar juna a tsakaninsu, rashin samun wadanda za su nemi shawara a wajensu ko yawan zurfin ciki, na daga cikin abin da zai sa wasu matan su fara shaye-shaye. Sakamakon yadda mijinta, kishiyarta, ‘ya’yan miji ko wasu abokan zama suke kuntata mata, ko sun tsangwami rayuwar ta, ta yi kokarin sanar wa iyaye ko makusantan ta halin da take ciki an kasa fahimtar halin da take ciki. Daga nan ne sai ka ga mata ta fara nemarwa kanta mafita tana shaye shaye, don dauke hankalinta daga damuwar da ke cinta a rai. Wata kuma tana fara wa ne da shan magungunan karin kuzari don ta samu zafin naman yin aikace aikacen gida nata ko na mutanen da take yi wa aikatau, daga nan kuma in jiki ya saba sai a zarce da harka.
- Duniya Na Fatan A Tabbatar Da Daidaiton Da Aka Cimma A San Francisco
- Hadarin Mota: NIS Ta Tabbatar Da Mutuwar Jamianta 4, 7 Sun Ji Rauni A Kano
Mu’amala da kawaye ko abokan zama na cikin gida masu shaye-shaye a boye shi ma yana janyo yawaitar wannan matsalar da bazuwar ta a cikin al’umma ba tare da an ankara ba. Wasu iyaye mata suna da sakacin shan magani barkatai idan suna da ciki, wanda hakan na iya taba jinjiri kafin ma ya zo duniyar an koyar da shi. Ko kuma mata masu ajiye magani barkatai a ko’ina suka ga dama, har yaro ya dauka ya fara sha ba tare da an lura ba.
Har wa yau, an gano cewa wani lokaci likitoci kansu suna janyo wanan matsalar ta hanyar hada mutum da maganin da jininsa ba zai iya dauka ba. A hankali kuma sai jikin mutum ya saba har ya ajiye kwalin maganin ko takardar likita ya rika zuwa Kemis yana saye, ko da bayan ya samu lafiya.
Na hadu da mutane da dama, wadanda a zahiri idan ka gansu cikin karamci da sutura ta mutunci ba za ka taba yi musu tunanin suna suna shaye-shayen magungunan kara kuzari da dauke damuwa ba. Kamar yadda wata abokiyar aiki da nake girmamawa ta taba yi min tayin shan wasu kwayoyi masu saurin dauke gajiya da sa a ji garau, bayan wani aikin rangadi na zagayen duba wasu ayyuka da muka yi. Saboda a ganinta shaye-shayen kwayoyin maganin cire gajiya ba wani abin damuwa ba ne, abu ne da ya zama gama gari, kuma ita ta saba, sai ta sha take barci.
Wadannan su ne hanyoyin na daga cikin sanannun dalilan da ke hadddasa matsalar shaye-shaye a cikin al’umma. Kuma duk da kokarin da Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ke yi, na fadakarwa da kama masu kasuwancin wannan harka a birane da lunguna, abin kullum sai kara ta’azzara yake yi.