… ci gaba daga makon jiya
5.Taimako ne ga daliban da basu gane abinda ake koya masu da sauri
Akwai lokacin da Malamai ko dai suna mantawa da wasu darussa ko maimaita su, irin hakan yana faruwa ne saboda babu tsarin yadda zasu koyar a aji.
Idan Malami ya tsara yadda zai koyar a aji tare da shi zai yi iyakar kokarinsa ya kauce ma mantawa da koyar da wani darasi ko kuma maimaita shi, adalilin da kan sa ana ba daibai damar zuwa sabon aji daga wanda suka kare.
Da Zarar aka ce an kammala shekarar karatu sabon Malamain da zai maimata ko duba yadda tsarin koyarwar yake, yin hakan zai taimaka ma shi kan abubuwan da suka dace yayi dangane da daliban da basu gane ko fahimci abubuwan da aka koya masu ba.
6. Samun karbuwa a matsayin Malamin da baraun koyarwar shi ke jan hankalin dalibai
Malamin daya tsara yadda zai koyar mai ma’ana zai iya jan hankalin dalibai wadanda za su nnuna kauna da sha’awar tsarin yadda yake koyar da su cikin gamsuwa.
Malami yana iya yin ko misalai da dalibai wadanda za su yi kamar yadda ya tsara a tsarin koyarwar sa ko yadda yake son su yi.Idan aka gane amfanin abin irin hakan lamarin zai dade ko su daliban za su dade suna tunawa da abin ko abubuwan da aka koya masu.
Ta wannan tsarin a matsayinka na Malamai za ka dora su kan tafarki maikyau akan muhimmancin tsarin yadda za a gabatar da wani abu ba sai lamarin daya shafi koyarwa ba kadai.
7. Tsarin da zai amfanar sosai
Matsayin na wanda zai jagoranci dalibanka zaka iya yin haka idan ka bullo da dabarun da za su taimaka maka tare da su.
Za ka kasance kai ne sanadiyar taimakawa dalibai wajen kammala ayyukan da aka basu ba tare da ka taimaka masu ba,ko ma ka taimaka abin ba zai daiki lokaci mai tsawo ba.
Tsarin koyar kasancewa yana tare da kai hakan yana taimakawa wajen gane ko gano yadda daliban suka fahimci darasin da ka koya masu, har ila yau hakan zai taimaka ma ka wajen sanin hanyar da za ka bullo ma su daliban da basu gane darasin da aka koya masu ba kamar yadda ake tsammani.
Ta wannan hanyar kana iya gane irin yadda suka fahimci darasin da ka koya masu, hakan yayin daidai da shit sarin koyawar naka da kuma su abinda daliban dake aji suka fi so.
8. Sa dalibai su kasance suna cikin halin da lamarin zai iya sa su farinciki tare da murna
Malamai sun dogara ne kan tafarkin muradan koyarwa kamar wasa,amfani da bidiyo, ko ziyartar wani kamfani.Irin hakan na sa dalibai su zama suna jran wani lamarin da basu sani ba,suna kuma kagarar sanin ko ganin menene.
Kana iya sa dalibanka su maida hankalinsu kan tattaunawa kan wani al’amari, wannan hanya ce manuniya dake nuna yadda abinda za ayi lokacin da za a sake haduwa wajen koyar da su.
Abinda zai ja hankalin dalibai masu koyon English Literature, lokacin da aka basu umarni na su yi bayani kan soyayyar da su kayi rashin nasara kan ta a Kwaleji.Kafin ma su fara, akwai tunanin da za su fara na fara ganin kimar wani muhimmin labarin soyayya na Romeo da Juliet!.