Mujallar “Science” ta kasar Amurka, ta gabatar da jerin manyan nasarori guda 10 da aka cimma a duniya, ta fuskar kimiyya da fasaha a shekarar 2025, a jiya Alhamis, inda “saurin ci gaban bangaren makamashin da ake iya sabuntawa” ya zama na farko a cikin jerin.
A ganin mujallar “Science”, a shekarar 2025 da muke ciki, ayyukan samar da makamashin da ake iya sabuntawa sun fara zarce na samar da makamashin gargajiya, inda kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a fannin jagorantar wannan sauyin salo.
Rahotanni na cewa kasar Sin na ta kokarin habaka bangarorin samar da allunan sola, da na’urorin sarrafa karfin iska, da baturan Lithium, ta yadda ta karfafa matsayinta na jagora ta fuskar samar da makamashin da ake iya sabuntawa, da fasahohi masu alaka da hakan. (Bello Wang)














