Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa, shekaru 23 a jere na mulkin dimokuradiyya sun haifar da ci gaba mai dorewa a Jihar Gombe da ma kasa baki daya, lamarin da ya taimaka wajen bunkasa rayuwar al’ummar jihar.
Kan hakan sai ya bukaci al’ummar Jihar Gombe su ci gaba da taka rawa wajen karfafa dimokuradiyya ta hanyar shiga a dama da su yadda ya kamata a harkokin zabe wadda ya ce yana ci gaba da ingantuwa a tsawon shekaru.
Ya yi kira ga al’ummar jihar su shiga a dama da su wajen jajirce a harkar shugabanci.
A wani sakon taya murna na alamta ranar ta dimokuradiyya ta 12 ga watan Yuni wanda Kakakin gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya fitar, Gwamna Inuwa ya ce dimokuradiyya ta samu wurin zama a kasar nan. Ya kuma bayyana jin dadin yadda aka gudanar da zabukan fid da gwani cikin nasara, yana mai kira ga al’ummar jihar su ci gaba da dabbaka wannan dattakun yayin da harkokin zaben 2023 ke dab da kankama.
Sai ya bukaci jama’a su yi amfani da damar ci gaba da rajistar masu kada kuri’a, musamman wadanda yanzu ne suka kai shekarun jefa kuri’a ko wadanda ba su yi rajistar ba a baya, don samun nasu katin zaben kuma su samu damar kada kuri’u wajen bayar da tasu gudunmawan gina kasa.
Ya yaba wa shugabannin jihar na yanzu da na baya, yana mai cewa kokarin da suka yi ya tabbatar da Jihar Gombe a matsayin dunkulalliyar jiha, “Mu a Jihar Gombe babu wata jayayya cewa, dimokuradiyya ta kawo ci gaba mai dorewa a jiharmu. Gwamnonin farar fula uku sun yi mulki, lamarin da ya share fagen shigowar tamu gwamnatin.
“Ina amfani da wannar dama wajen yabo da jinjina ga tsofaffi da shugabanninmu masu ci, wadanda suka ba da gudunmawa wajen karfafa dimokradiyya da harkokin siyasarmu.
Don haka ina kira a gare mu, mu kara jajircewa wajen gina kasa, mu kara hada kai wajen tunkarar matsalolinmu ta hanyar jajircewa ga addu’o’i. Dole ne mu sani cewa aikin gina kasa alhakki ne a kanmu baki daya,” a cewar Gwamnan.