Wani haɗarin mota da ya faru a yau Lahadi a hanyar Lokoja-Obajana ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19, yayin da wasu 8 suka jikkata.
Sakataren FRSC na jihar, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da cewa haɗarin ya faru ne sakamakon gudun da ya wuce ƙima. Mota bas da wata babbar mota sun yi karo da juna a Gada biyu, inda yara 5 suka ƙone har lahira.
- Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Kano – FRSC
- Kashi 25 Kawai Na Motocin Da Ke Nijeriya Suke Da Inshora – FRSC
“Mutane 27 ne haɗarin haɗarin ya rutsa da su, 8 kacal suka tsira,” in ji Tsukwam. An kai wadanda suka tsira asibitin Fisayo a Obajana don samun kulawa.
FRSC ta yi kira ga direbobi su guje wa gudu da ya wuce gona da iri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp