Shugaban kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) reshen Jihar Kaduna, Rabaran John Joseph Hayab, ya bayyana cewa sun biya kudin fansa Naira miliyan 250 domin a sako dalibai 121 na makarantar sakandare ta Bethel Baptist da aka yi garkuwa da su a watan Yuli 2021.
Rabaran Hayab ya bayyana haka ne a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Uba Sani a Kaduna.
Ya kuma bayyana cewa Treasure Ayuba, dalibin Bethel na karshe da ya tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su kimanin mako daya da ya wuce,ya musanta rade-radin da ake na cewar dalibin ya nuna sha’awar zama a hannun maharan.
Shugaban na CAN ya bayyana cewa an yi kokarin ganin an sako Treasure, ciki har da aika kudin fansa ga maharan har sau biyu, ya kara da cewa jimillar kudaden da aka biya domin a sako su a karshe ya kai Naira miliyan 250.
“A yau, mun taru a nan don nuna godiya. Muna maraba da dawowar Treasure Ayuba, dalibi na karshe da ya rage a hannun ‘yan bindiga na makarantar sakandaren Bethel Baptist da ke nan Kaduna.
Ya bayyana irin kalubalen da ‘yan uwan Treasure suka fuskanta wajen ganin an sako shi da kuma sace-sacen da aka yi a lokacin da aka kai kudin fansa.
Da yake mayar da martani, Gwamna Uba Sani ya ba iwa Treasure Ayuba tabbacin goyon bayan gwamnatin jihar tare da bayyana cewa ana daukar matakan inganta lafiyar dalibai a makarantun jihar.
Uba Sani ya ce kafa kwamitocin tsaro a makarantu, tura jami’an ‘yan banga na Kaduna (KADVIS), da kuma tabbatar da harabar makarantu ta hanyar gina shinge na daga cikin matakan tabbatar da tsaron dalibai da kuma inganta yanayin karatu.
“Mun dauki matakin kare makarantunmu da kuma tabbatar da cewa yaranmu sun samu ilimi a yanayi mai kyau. Za mu kafa kwamitocin tsaro a dukkan makarantu, mu tabbatar da tura jami’an tsaro na KADVIS (Kaduna Vigilance Service) zuwa dukkan makarantunmu, tare da tabbatar da tsaron makarantunmu ta hanyar gina katanga a kewayen makarantun, da sauran matakan da za mu dauka,” in ji shi.