Gwamnan jiharsu Bauchi, Bala Muhammad ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta ciwo bashin cikin gida na Naira biliyan 100 domin gudanar da ayyukan raya jihar domin cika alkawuran da suka dauka a lokacin yakin neman zabe.
A cewar gwamnan a cikin wannan adadin zuwa yanzu jihar ta kashe kusan naira biliyan 90 wajen gudanar da ayyukan more rayuwar al’umma.
- Gwamna Nasir Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Naira Biliyan 250 Ga Majalisar Dokokin Kebbi
- Labarin Rasuwar Janar CG Musa Ba Gaskiya Ba Ne – Rundunar Tsaron Nijeriya
Ya ce: “Mun ciyo bashin Naira biliyan 100 kuma zuwa yau gudanar da ayyukan more rayuwa kawai sun kusa kaiwa biliyan 90. Mu ba barayi ba ne, ba muna nan domin daukar wani abu daga cikin tsarin ba ne. Za mu tabbatar ko wane sisin kwabo an kashe shi a inda ya kamata.”
Ya kara da cewa, “Tabbas akwai bukatar mu ajiye wani abu domin bangaren ilimi da lafiya. Muna adana daga dan kason da muke samu daga gwamnatin tarayya, domin mu bar kudaden bashin wajen samar da ayyukan more rayuwa zalla.”
Gwamna Bala wanda ke magana yayin da ke bude zaman majalisar zartarwar jihar a ranar Laraba, ya hori kwamishinoninsa da su kasance jakadu na kwarai kana su sanya ido kan yadda ake tafiyar da harkokin kudade a ma’aikatunsu.
Gwamnan ya sanar da aniyar gwamnati na gudanar da babban taro kan ilimi da zuba hannun jari, yayin da jihar ke aiki tukuru domin janyo hankalin masu zuba hannun jari ta yadda jihar za ta samu karin tagomashi.
Gwamnan ya nemi kwamishinonin da su ci gaba da yin aiki domin kyautata jihar jihar tare da sadaukarwa domin samar da ci gaba mai ma’ana.