Hedikwatar rundunar tsaron Nijeriya ta yi watsi da jiya-jitar cewa babban hafsan hafsoshin tsaron kasar nan, Janar CG Musa ya mutu.
Labarin rasuwar ya bulla ne a kafafen sada.
- Zaben Kano: ‘Yansanda Da Masu Zanga-zanga Sun Yi Arangama A Kano
- Yadda Aka Farmaki Hedikwatar ‘Yansanda A Adamawa -Kwamishinan ‘Yansanda Ya Mayar Da Martani
Kakakin rundunar tsaron Nijeriya, Brigadiya Janar Tukur Gusau ne, ya yi bayanin cewa jita-jitar ba gaskiya ba ne kuma Janar CG Musa ya dawo Nijeriya daga bulaguron aiki da ya kai kasashen waje.
Tuni kuma babban hafsan ya isa ofishinsa yau da safe don ci gaba da ayyukansa kamar dai yadda ya saba.
Saboda haka rundunar tsaron ta yi tir da wannan rahoto na kanzon kurege da aka buga, inda ta ce ko kadan babu sanin ya kamata a cikinsa.
Don haka ta nemi manema labaru su rinka bincikar gaskiyar labari kafin su wallafa a shafikansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp