A watan farko da shigowa sabuwar shekarar 2023 (wato janairu), ‘yan kasuwa a jihar Gombe, waiwaye suka yi a shekarar da ta gabace ta, wato 2022 inda da yawa sukayi kukan cewa, sun dandana kudar su a shekarar, saboda, hauhawar farashi a kan duk kayayyakin kasuwanci, musamman abinci da kayan masarufi da kuma rashin tsaro, suna mai kukan cewa ‘’kar Allah ya sake maimaita mana irin wannan masifa’’.
A wani zagaya, da ‘yan jarida suka yi a ranar Litinin din wannan makon, ta ji wasu da dama cikin yan kasuwa, manya da kanana, suna kukan cewa, ‘’gwamnatin Buhari ba ta’ yankasuwa ba ce, domin mu bamu taba fuskantar rayuwa kamr a karkashin mulkin shi (Buhari) ba’’.
- Tsokaci Kan Dukan Da Wasu Maza Ke Wa Matansu
- An Yi Gwanjon Rigar Da Pele Ya Buga Kofin Duniya Na Karshe Da Ita
Fitaccen dan kasuwan kayayyakin gini, kuma shugaban Sabham (Nig) Ltd, Gombe, Alhaji Sabo Adamu, ya ce, ai sake bada umurnin a bude kan iyakokin kasar bayan rufe su, na daya daga cikin abubuwan da suka jawo hauhawar farashi a Najeriya.
‘’Don haka, Gwamnatin ta sake tunani a kan lamarin ta kuma bada unurni a rurrufe bodojin, saboda hakan zai sa ‘yan kasa su dukufa wajen bunkasa kayayyakin cikin gida, kaya da abinci su yawaita, kuma za’a samu saukin rayuwa’’ inji shi.
A hira da Babban Manajan sanannen kamfanin hada – hadar dilolin atamfofi da kayayyakin amfanin yau da kullum na maza da mata da yara, wato SAN HUSSEIN SUPER MARKETS Gombe, Alhaji Muhammad Umar Kawu, Shi nuna godiya ya yi ga Allah da shigowar sabuwar shekarar 2023 lami lafiya.
Dangane da tsadar rayuwa da ‘Yan Najeriya suke ta kuka a kai kuwa, sai Alhaji Muhammad Kawu yace, ‘‘mu koma ga Allah, duk da mun san irin halin da muka shiga sai adu’a, ita ce kawai mafita ‘’.
Sai ya shawarci ‘Yan Jihar ta Gombe, da ma ‘yan kasa baki daya, da su rinka yi wa Shugabanni Addu’a, maimakon aibantasu , yana kuma matukar hamdala da kamfanonin SAN HUSSEIN, da suka kara bunkasa saboda sassautawa kwastomomin su farashin kayayyaki, ‘‘Don haka, ina fata ‘Yan kasuwa, takwarorin mu, su tausayawa talakokin mu wajen rage tsadar kayayyakin su saboda yin haka ce zai sa suga alheri da ci gaba a kasuwancin su’’.
Manajan kuma, sai ya yi fatan Allah Ya kawo wa Najeriya ci gaba a wannan sabon shekara ta 2023, da kuma adu’ar Allah Yasa zabubbuka masu zuwa, za’a yisu cikin lumana da kwanciyar hankali. Kusan kashi 75 cikin dari (75%) da aka zanta da su, sun dora laifin ne akan Gwamnatin Shugaba Buhari suna nanata cewar ‘’ kar Allah Ya sake maimaita mana’’.