Shugaban kwamitin hana kwacen waya da yaki da miyagun kwayoyi da fadace-fadacen daba da gwamnati Kano ta kafa a watanni 21 da suka wuce, Janaral Gambo Ahmed mai Addau mai ritaya, ya bayyana ce wa yanzu haka wannan kwamiti ya gano cibiyoyi 52 da ake aikata laifuka a daukacin Jihar Kano.
Ya kara da cewa yanzu haka bisa umarni da amincewar gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wannan kwamiti ya dauki matasa 1,050 aiki, wanda kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na Kano, Ibrahim Umar ya kaddamar a madadin gwamnan, domin hada hannu da jami’an ‘yansanda da na NDLEA da cibil defence, da na leken asiri da na farin kaya (DSS), da ‘yan bijilanti da sauransu, domin murkushe wannan mummuna aiki na fadan daba da kwacen waya da harkar miyagun kwayoyi a Kano.
- ‘Yansanda Sun Kama Matasa 51 da Ake Zargi Da Faɗan Daba A Kano
- An Nemi A Kafa Dokar Ta-ɓaci Kan Masu Ƙwacen Waya
Janar Mai Addau ya bayyana cewa yanzu haka gwamnatin Kano ta samar da motoci da ababan hawa don wannan aiki kimanin 100 da kuma alwashin bayar da duk abun da wadannan zaratan matasa ke bukata don yin wannan aiki na tsare lafiyar al’ummar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp