Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce jam’iyyar ADC da yake ciki yanzu ta shirya tsaf domin fuskantar jam’iyyar APC mai mulki.
Ya ce wannan yunƙuri na neman kawo sauyi ne saboda irin halin da ake ciki a ƙasar.
- Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Tsawon Kwana 60 Da Hamas – Trump
- Zambiya Ta Kaddamar Da Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana Mafi Girma
Malami, wanda ya riƙe muƙamin minista a lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta jefa talakawa cikin mawuyacin hali da ƙunci wanda ba za a iya misalta shi ba.
A hirarsa da BBC, Malami ya ce sun fito fili domin su ƙalubalanci gwamnati mai ci saboda yadda abubuwa suka taɓarɓare, musamman ɓangaren tsaro da tattalin arziƙi, da sauran matsalolin da ke addabar al’umma.
Ya ce idan wata gwamnati ta zo da manufofin da ke cutar da jama’a da jefa su cikin wahala, to dole a haɗa kai domin ɗaukar mataki, domin kawo gyara da tsari mai amfani ga rayuwar mutane.
Malami ya ƙara da cewa suna da cikakken shiri da azama don fuskantar APC da kuma kawo canji mai ma’ana a Nijeriya.
“Mun yanke shawarar fuskantar gwamnati mai ci domin yaƙi da matsalolin tsaro da yunwa, tare da mayar da Nijeriya kan hanyar da ta dace,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp