Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da tabbacin cewa ba za ta bari shirin ilmantar da ‘ya’ya mata na AGILE ya gurbata tarbiyyar yara a makarantun jihar ba.
Gwmnatin ta ce ta yi watsi da wasu akidun shirin AGILE tare da rungumatar manufofin shirin na gyara makarantu da bai wa malamai horo a kan ilimi.
- Bayan Zantawa Da Sin Lokaci Ya Yi Da Philippines Ta Gane Kuskurenta
- Majalisar Dokokin Sokoto Ta Amince Da Bukatar Gwamna Aliyu Na Kafa Jami’an Tsaron Jiha
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin ilimi na majalisar dokokin Jihar Kaduna, Barista Mahmud Lawal a wata zantawa da ya yi da manema labarai a zauren majalisar jim kadan bayan Gwamna Uba Sani ya gabatar da kasafin kudin jihar.
Barista Lawal wanda aka fi sani Bola Ige, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta yi iya bakin kokarinta wajen tabbatar da cewa shirin AGILE bai gurbata tarbiyyar ilimin mata ba.
Bola Ige, wanda shi ne dan majalisar dokoki mai wakiltar mazabar karamar Hukumar Zariya, ya ci gaba da cewa, “Daga cikin manufofin AGILE mun dauki guda uku, mun yi watsi da sauran, mun dauki manufarsu na gyara makarantu da horas da malamai da ba da tallafin kayan karatu. Amma kudirinsu na bai wa yara mata tarbiyya irin nasu da sauransu mun yi watsi da su. Mun tabbatar da cewa shirin na AGILE mu a Jihar Kaduna ba za mu bari ya gurbata mana tarbiyyar ilimin mata ba ” in ji shi.
Shirin AGILE na da nufin habaka ilmin zamani na ‘yan mata daga karamar makaratun sakandaren zuwa babba, inda ma har ake ba su wani ihisani.
Sai dai wasu masu nazari da suka yi sharhi a kai sun ce shirin babu abin da yake yi sai gurbata tarbiyya da kokarin sanya daliban bujire wa iyaye da gurbata ka’idodi da tarbiyar addini da ta al’ada.