Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, sun soki matakin Shugaba Bola Tinubu na ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas.
A ranar Talata ne Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar, inda ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, da mambobin majalisar dokokin jihar.
- Gwamnatin Nasarawa Ta Fara Aikin Sabunta Asibitoci 58 Don Inganta Lafiyar Jama’a
- Jami’i: Jiragen Saman Kasar Sin Za Su Bunkasa Sashen Sufurin Jiragen Afirka
Wannan mataki ya janyo suka daga shugabannin jam’iyyun adawa da masana doka, inda suka ce ba ya saɓa dokokin kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa wannan mataki ba bisa doka aka zartar da shi ba, yana mai kira ga Shugaba Tinubu da ya janye shi tare da dawo da zaɓaɓɓun shugabannin jihar kan kujerunsu.
Atiku da sauran jiga-jigan adawa sun buƙaci Majalisar Dokoki na ƙasa da su yi watsi da dokar, domin a cewarsu, matakin ya saɓa wa dimokuraɗiyya kuma yana iya zama barazana ga tsarin mulkin ƙasa.
Mece ce Dokar Ta-ɓaci?
Dokar ta-ɓaci tana bai wa shugaban ƙasa damar ɗaukar matakan gaggawa a wani yanki na ƙasa idan ana fuskantar barazanar tsaro ko zaman lafiya.
Sai dai kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi cewa dole ne a bi tsari na doka kafin a aiwatar da hakan.
Mece Ce Ma’anar Wannan Mataki A Ribas?
Ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas yana nufin Gwamnatin Tarayya ta ƙwace ikon jihar, kuma hakan na iya kawo cikas ga harkokin siyasa da ci gaban jihar.
Masana doka da ‘yan adawa na ganin cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulki, kuma yana iya zama wata hanya ta take haƙƙin masu mulki da aka zaɓa a jihar.
Tun bayan ɗaukar wannan mataki, ake samun martani daga ‘yan siyasa da ƙungiyoyi masu rajin kare dimokuraɗiyya, inda suke kira da a janye dokar domin kare doka da tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp