- …Nijeriya Na Da Karfin Tuwon Maido Bazoum Cikin Sa’o’i 24 -Dakta Blessing
- …Dattawan Arewa Sun Sake Rokon A Dage Wa Kasar Takunkumai
Shugaban Nijeriya kuma shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa suna bibiyar sojojin da suka yi junyin mulki a Nijar su ga iya gudun ruwansu.
Tinubu ya ce ECOWAS ba za ta lamunci gwamnatin soja ba a daidai lokacin da ake mulkin dimokuradiyya.
Ya jinjina wa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afirka (ECCAS) bisa irin gudunmuwar da suke bayarwa kan batun juyin mulkin kasar Nijar.
Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakancin wakilin Shugaban Ali Bongo Ondimba kuma ministan harkokin wajen kasar Gabon, Mista Hermann Immongault, a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Talata.
Shugaban ya kara da cewa sakon na musamman na goyon baya da hadin kai daga Shugaba Bongo, wanda ya zama shugaban ECCAS, yana mai bayyana cikakken goyon bayan kudurorin ECOWAS kan juyin mulki a Nijar, ya kara tabbatar da cewa juyin mulkin sojoji a daidai lokacin da ake mulkin dimokuradiyya ba abu ne da za a amince da shi ba a Nahiyar Afirka.
“Ina godiya da irin hadin kai da goyon bayan da Shugaba Bongo ya bayar kan halin da ake ciki a Nijar. Muna kokarin yadda za a warware lamarin cikin ruwan sanyi ba tare da matsala ba. Muna da mutane masu yawa da ke shiga tsakani.
“Na fahimci tsoron da mutanenmu ke yi kan kowane irin matakin soja. Muna aiki don kiyaye takunkumin da aka kakaba kuma muna bin su domin mu ga iya gudun ruwansu.
“Muna farin cikin sanin cewa ECCAS na tare da mu a kan wannan lamari. ECOWAS ba za ta amince da mulkin soja ba a daidai lokacin da ake mulkin dimokuradiyya,” in ji shi.
…Nijeriya Na Da Karfin Tuwon Maido Bazoum Cikin Sa’o’i 24 -Dakta Blessing
Har iya yau, wata kwararriyar masaniyar harkokin tsaro, Dakta Blessing Agbomhere ta bayyana cewa Nijeriya a karkashin Shugaban Kasa Tinubu kuma shugaban ECOWAS na da karfin tuwon maido da hambararren Shugaban Kasan Nijar, Mohammed Bazoum kan kujera Cikin sa’o’i 24.
Agbomhere ta bayyana kaduwarta da takaicin yadda wasu ‘yan Nijeriya ke nuna adawa da shirin ECOWAS na mayar da mulkin farar hula a Jamhuriyar Nijar.
A cewarta, fargabar da wasu ‘yan Nijeriya ke nunawa kan shiri da rundunar sojin kasar ke yi na tunkarar gwamnatin sojojin juyin mulkin Nijar cikin kankanin lokaci lamari ne da ke nuni da rashin kishin kasa da kuma kin daukar matakin da ya dace daga gwamnatin da ta shude wacce tun farko ta yi fafutuka wajen dakile ’yan ta’adda da ‘yan bidiga da suka addabi wasu sassan kasar nan.
Ta jaddada cewa ba gaskiya ba ne da ake cewa nuna irin halin da sojojin Nijeriya a karkashin jagorancin Shugaba Tinubu ke ciki, wanda ya yi imanin cewa yana da dukkanin bayanai da dabarun da ake bukata don gudanar da aiki cikin gaggawa da samun nasara a Nijar ba tare da bata lokaci ba da kuma haifar da hasarar da ba gaira ba dalili ga sojojin kasar.
“Shugaba Tinubu ya shirya tsaf don sake dawo da martabar Nijeriya, dole ne mu mara masa baya don sake mayar da Nijeriya matsayinta na jagoran kasashen Afirka “, in ji shi.
Sai dai ta bayyana cewa tattaunawa ita ce hanya mafi dacewa wajen warware rikicin siyasa a Nijar, tana mai jaddada cewa bai kamata Nijeriya ta yi watsi da alhakkin da ya rataya a wuyanta na wanzar da mulkin dimokuradiyya a yankin Afirka ta yamma ba, ta hanyar daukar matakan soja, kamar irin rawar da ta taka a tsawon shekaru a kasashen Laberiya da Sao Tome da Sierra Leone da Cote D’Iboire, sannan za ta ci gaba da taka rawa wajen kare martabar mulkin dimokuradiyya da zaman lafiya a yankin.
…Dattawan Arewa Sun Sake Rokon A Dage Wa Kasar Takunkumai
Sai dai kuma kungiyar dattawan arewa (NEF) ta sake shawarci Shugaba Tinubu wanda shi ne shugaban ECOWAS ya gaggauta dage wa kasar Nijar takunkumai da aka kakaba mata.
A dai ranar 4 ga Agusta ce, Nijeriya ta rufe dukkan iyakokinta da kasar Nijar da kuma yanke wutar lantarki sakamakon kin mayar da mulki ga hambararren shugaban kasan, Bazoum da sojojin juyin mulki suka hambarar da gwamnatinsa a ranar 26 ga Yuli.
Da yake jawabi a taron manema labarai a Abuja, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na kungiyar NEF, Dakta Hakeem Baba Ahmed, ya ce, “Ya kamata Nijeriya ta cire duk wani takunkumi da sauran matakan da ta dauka na tilasta wa gwamnatin sojojin juyin mulki.”
Ya bukaci Tinubu da ya tabbatar da tsaron lafiyar hambararren shugaban kasan, Bazoum da iyalansa da kuma maido da tsarin mulkin dimokuradiyya, su kasance muhimman abubuwan tattaunawa.
Kungiyar NEF ta yi watsi da amfani da karfin soja a kasar, inda ta kara da cewa matakin zai kara dagula lamarin ne kawai.
“Ya kamata a yi watsi da amfani da karfin soja a kan Nijar. Da wuya a cimma manufofin maido da tsarin mulkin dimokuradiyya idan aka yi amfani da karfin soja. Hakan zai kara dagula lamarin tsaro da ke addabar al’ummar yankin kasashen ECOWAS,” in ji shi.