Kamfanonin sufurin jiragen sama na kasashen waje da ke zirga-zirga zuwa Nijeriya sun bayyana bacin ransu dangane da rashin biyansu kusan kashi 90 cikin 100 na kudadensu da suka makale a wanda ya kai dala miliyan 783.
Kamfanonin jiragen sun bayyana haka ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin sufurin jiragen sama karkashin jagorancin ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo a Jihar Legas.
- Wadanne Damammaki Da Aka Samu Cikin Abubuwan Da Aka Nuna A Karon Farko A Duniya A CIIE?
- Burin Sin Na Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya Bai Sauya Ba
Bayanai daga kungiyar sufurin jiragen sama ta kasa da kasa, sun nuna cewa, ya zuwa watan Agustan wannan shekara ta 2023, kudaden da kamfanonin sufurin jiragen sama na kasashen waje da Nijeriya ta gaa biya sun kai dala miliyan 783.
Duk da kokarin shawo kan lamarin da gwamnatin tarayya ta yi a baya-bayan nan, kamfanonin jiragen saman sun ce har yanzu ba su kai ga samun kaso mai yawa na kudaden ba.
Makonni biyu da suka gabata Shugaba Tinubu, ya yi alkawarin biyan wasu bankunan kasuwancin kasar nan kimanin dala biliyan bakwai na kudaden waje da ke hannun gwamnatin tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp