Gwamnatin Tarayya ta ce tana aiki ba dare ba rana don magance matsalolin tsaro da ake fama da ita a halin yanzu, ta hanyar yaki da rashin tsaro zuwa matsugunan masu aikata laifuka a fadin kasar nan.
Ministan ya ce a cikin makon da ya gabata, an kawar da ‘yan fashi, masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan bindiga da dama, ko kuma aka kama su.
- Jami’an Tsaro Sun Kama Ɗan Bindigar Da Ake Zargi Da Kashe Nabeeha
- Zaben Cike Gurbin Makera: ‘Yan Takara Sun Yi Wa Liman Mubaya’a
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris Malagi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a Abuja.
“Ba zai yiwu a yi watsi da gaskiya a wannann lokaci na kalubalen da muka samu kanmu a matsayinmu na al’umma: illar hauhawar farashin kayayyaki a kan kasafin kudin mutane da na gida, da kuma barazanar tsaro a sassan kasar nan.
“Amma wannan wani bangare ne na labarin. Kamar yadda muhimman matakai daban-daban da gwamnatin tarayyar Nijeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ke dauka na tunkarar duk wadannan kalubalen.
“Mun amince da aiki da kuma nauyin kulawar da Gwamnatin Tarayya ta rataya a wuyan kowane dan Najeriya, a tsakanin shekaru, jinsi, addini, kabila, da zamantakewa,” in ji shi.
Kashe-kashen Filato
Ministan ya ce hukumomin tsaro na taka tsan-tsan wajen tunkarar matsalolin da suka sake kunno kai a Jihar Filato da sauran yankunan da ke fama da rikici a daidai lokacin da shugaba Tinubu ya yi alkawarin samar da zaman lafiya a duk fadin kasar.
Ya kuma ba da tabbacin cewa za a gurfanar da masu aikata kisan-kiyashi da tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar nan a Filato.
“Hakika rikicin da ya sake kunno kai a Jihar Filato abin takaici ne matuka, kuma muna ba da tabbacin cewa duk wadanda suka haddasa tashin hankali a can da kuma ko’ina a fadin kasar nan, an gurfanar da su a gaban kuliya. Za a yi adalci, kuma za a maido da zaman lafiya a dukkan al’ummomin da abin ya shafa.
“Muna jinjina wa jiga-jigan jami’an tsaro da na leken asiri wadanda ba sa barin wani abu don tabbatar da cewa muna cikin koshin lafiya a gidajenmu da kan manyan tituna, kuma masu aikata laifuka ba su da sararin shakar numfashi,” in ji Ministan.