Kungiyar Masu Shuke-shuken Kayan Lambu ta Kasa (POFON) ta bayyana cewa, tana bukatar karin hekta 500,000, domin noman kwakwar manja.
Har ila yau, ta sanar da cewa; tana da wannan bukata ce, domin kara bunkasa noman kwakwar manjan tare da samar da wadatuwarta, duba da karin bukatar da ake da ita a fadin kasar baki-daya.
- NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai
- Ana Ci Gaba Da Caccakar El-rufai Kan Kalamansa Game Da Tsaron Kasa
Shugaban kungiyar na kasa, Mista Emmanuel Ibru, ya bayyana hakan ne a hirar da aka yi da shi, kan batun yadda kungiyar za ta samar da wadatacciyar kwakwar manjan a Nijeriya da kuma batun daidata farashinta a daukacin fadin kasar.
Shugaban ya bayyana cewa, kungiyar za kuma ta daidai ta farashin kwakwar, har zuwa karshen shekarara; hatta a cikin kowace kakar noma a kasar.
“A daukacin Nahiyar Afirka, Nijeriya ce kan gaba wajen noman kwakwar manja, sannan kuma ita ce ta biyar a noman kwakwar manjan a dukkanin fadin duniya,” in ji Ibru.
Ya kara da cewa, saboda haka; akwai bukatar a kara yawan hektar noman kwakwar manjar zuwa hekta akalla 500,000, domin cike gibin bukatar da ake da ita a kasar nan tare kuma da kara bunkasa nomanta a Nijeriya baki-daya.
Shugaban ya ci gaba da cewa, har yanzu a Nijeriya ana ci gaba da fuskantar samun gibi wajen samar da kwakwar, sai dai ya bayyana cewa; sama da shekara 10 zuwa shekara 15 kungiyar ta POFON ta yi namijin kokari, wajen kara yawan noman kwakwar a daukacin fadin kasar.
A cewarsa, manyan gonaki a kasar da ke nomanta kamar irin su, Presco da kuma Okomu sun kara dage damtse wajen zuba hannun jari da kuma kara fadada gonakin noman kwakwar manjan kwarai da gaske.
Haka zalika, shugaban ya bayyana cewa; wasu sabbin gonaki kamar irin su Dufil, Saro Africa da sauransu, sun shiga Jihar Edo tare da zuba hannun jari a fannin na noman kwakwar.
“Saro Africa, ta samar da hekta 20,000 a Jihar Edo, Wilmar ta mallaki hektar noman kwakwar ta PZ Wilmar, inda yanzu yake kokarin sake noma wasu hektocin guda 8,500, wanda hakan zai bai wa gonar damar hekta guda 50,000 a cikin kasar.
“Gonakin JB, su ma sun kara zuba hannun jarinsu a Jihar Kuros Ribas, inda a yanzu suke kan kara samar da wasu hekta guda 10,000, ta noman kwakwar manjan a Jihar Ondo,” a cewar shugaban.
Ya ci gaba da cewa, akwai kuma wata gonar ta noman kwakwar manjan da ke ci gaba da kara zuba hannun jarinsu.
“Kimanin shekaru takwas da suka gabata, jimillar gundarin manjan da ake samarwa a kasar, a wannan yankin ake samar da shi wanda ya kai daga tan 900,000 zuwa tan miliyan daya,“ in ji shugaban.
“Ya zuwa yanzu, mun samu nasarar kara yawansa zuwa kimanin daga miliyan 1.4 zuwa miliyan 1.5, wanda hakan ya nuna cewa; ya kai kashi 50 na manjan da aka sarrafa,” in ji Ibru.
Koda-yake dai, shugaban ya sanar da cewa; ana ci gaba da samun gibi a samar da kwakwar manjan a kasar, amma kungiyar na kan yin aiki da wasu hukumomin gwamnati, domin samar da wani jadawalin kara bunkasa fannin a kasar nan da kuma kara zuba kudi a bangaren.
Ya yi nuni da cewa, jadawalin, ba wai kawai manyan masu noman kwakwar manjan ba ne, hatta su ma kananan monoma a fannin, za su yi matukar amfana.
Da yake yin tsokaci kan tsadar manjan a fadin wannan kasa, Ibru ya bayyana cewa; kungiyar na ci gaba da yin kokari wajen daidaita farashinsa kwarai da gaske.
“A wannan kasa da muke ciki, sau biyu ake yin noman kwakwar manja a shekara, yadda idan aka girbe ta da yawa, farashin nata ke raguwa daga baya kuma farashin ya kara tashi,“ a cewar shugaban.
Haka zalika, ya sanar da cewa; ‘ya’yan kungiyarmu na matukar kokari wajen ganin sun daidata farashin manjan a fadin kasar baki-daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp