Mukaddashin Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya yi kira da a kara wa rundunar sojojin kasa kasafin kudi don ta samar da gidaje ga sojoji.
Da yake magana yayin ziyarar ta’aziyya daga Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji a Abuja, Oluyede ya bayyana cewa rundunar na daukar sojoji kusan 15,000 duk shekara amma ba ta da isassun gidaje da za ta ba su.
- Kasar Sin Ta Yi Alkawarin Tabbatar Daidaiton Tsarin Masana’antu Da Na Samar Da Kayayyaki A Duniya
- Netanyahu Ya Amince Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Da Hezbollah
Ya yi gargadin cewa matsalar za ta kara tsananta idan an samu zaman lafiya kuma sojoji suka koma bariki.
Ya yi kira ga Majalisar Dattawa da ta tallafa wa rundunar wajen magance wadannan matsaloli a kasafin kudin shekara mai zuwa don inganta tsaro a kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp