Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewar gwamnatin tarayya na fuskantar kalubale sosai wajen tafiyar da kasar nan lura da dimbin matsalolin da suka addabe ta.
Yayin da yake karbar ministan Denmark, Dan Jorgensen da ya ziyarci fadar shugaban kasa da ke Abuja, Shettima ya ce ya zama wajibi su lalubo hanyoyin tunkarar wadannan matsalolin da ke yi wa ci gaban Nijeriya tarnaki.
- Yadda Ma’aikatan MDD A Nijeriya Suka Girmama Takwarorinsa Da Aka Kashe A Gaza
- Akwai Bukatar Sin Da Amurka Su Hada Hannu Domin Kyautata Dangantakarsu
Shettima wanda ya bayyana shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin mai ilimi da kuma kwarewar da ake bukata wajen fitar da Nijeriya daga rana, ya ce yana da kwarewar da ake bukata na jagorancin kasar nan domin samar mata da ci gaba.
Mataimakin shugaban ya ce duk da yake man fetur na sahun gaba wajen taka rawa nan da shekaru 10 masu zuwa, a matsayinsa na ginshikin tattalin arzikin Nijeriya, sai dai a halin yanzu karsashinsa na iya dakushewa a shekaru masu zuwa, abin da ya sa ya zama wajibi su sake tunani domin lalubo wasu hanyoyin da kasar nan za ta dogara da su.
Shettima ya ce wannan ya sa suka fara mayar da hankali wajen zuba jari a bangarorin fasaha da makamashi da ba ya gurbata muhalli da kuma wasu bangarori na daban.
Shettima, ya bayyana irin hasken da wannan bangare na fasaha yake da shi da kuma bangaren zuba jari ta hanyar makamashin da baya gurbata muhalli, wanda ya ce zai taka rawa sosai wajen karkatar da akalar tattalin arzikin Nijeriya.