Gwamnatin kasar Amurka ta bayyana cewa ba ta goyon bayan duk wani dan takara ko jam’iyya a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun da ranar 11 ga watan Maris a Nijeriya.
Mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin Afirka, Molly Phee ita ta bayyana hakan yayin da ta kai ziyara ga shugabannin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a Abuja.
- Za A Kira Taruka Biyu A Farkon Wata Mai Zuwa
- Kotu Ta Yanke Wa Mutum 2 Hukunci Kisa Kan Kashe Ma’aurata A Ondo
Ta ce damuwar Amurka a matsayinta na mai habaka dimokuradiyya shi ne, karfafa gudanar da zabe cikin nasara wanda zai kasance sahihi kuma mai cike da zaman lafiya da lumana.
Phee ta ce: “Tun a shekarar 1999, Nijeriya ta ci gaba da yin gyare-gyare wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya. Kuma a yanzu, a karkashin jagorancin shugaban hukumar INEC tare da tawagarsa, dukkan ‘yan Nijeriya za su iya amincewa da sahihancin zabe mai zuwa.
“Ina so in jaddada mahimmancin gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, kuma ina so in jaddada cewa kowane dan kasa, kowane mai ruwa da tsaki, duk jam’iyyar da ke cikin zabe na da hakki kafin zabe, lokacin yakin neman zabe, lokacin zabe da kuma bayan zabe kasancewa cikin zaman lafiya da lumana. Yana da matukar muhimmanci, domin kalubale ne da muka fuskanta a kasarmu.”
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, yayin da yake mayar da martani ya nanata cewa hukumar ba ta siyasa ba ce, kuma ba ta da dan takara da take mara wa baya.
Ya kuma ba da tabbacin hukumar zabe za ta tabbatar da zabin da ‘yan Nijeriya suka yi a zaben.
Yakubu ya kara da cewa: “Kamar dai kasar Amurka, hukumar ba jam’iyyar siyasa ba ce. Ba mu da ‘yan takara kuma za mu mayar da hankali ne kawai kan tsarin.
“Zabi na mutanen Nijeriya ne, kuma hukumar za ta tabbatar da zabin da ‘yan Nijeriya suka yi. Mun himmatu wajen tabbatar da sahihin zabe a 2023.
“A zahirin gaskiya, Amurka tana sha’awar dimokuradiyyar Nijeriya, ita ma Nijeriya tana sha’awar dimokuradiyyar Amurka. Na fadi wannan a Washington ga wadanda ba su ji ni ba. Ina so in sake maimaitawa. Idan Amurka ce babbar dimokuradiyyar shugaban kasa a duniya, wace kasa ce ta biyu mafi girman dimokuradiyya a duniya? A zahiri Nijeriya ce.
“Bisa kiyasin yawan al’ummar Nijeriya nan da shekaru biyu masu zuwa, wa ya san mu ma za mu iya zarce Amurka gaba daya wajen dimokuradiyya mafi girma a duniya. Don haka, muna sha’awar tabbatar da karfafa dimokuradiyyarmu. Babu wani tsarin gwamnati da ya fi tsarin.