Shugaban kwamitin tsaftace ayyukan ‘yan masana’antar kannywood wanda hukumar tace fina-finai da dab’i ta Jahar Kano ta kafa domin tabbatar da ana bin dokokinta sau da kafa Tijjani Asase ya bayyana cewa kwamitinsu ya samu nasarori da dama tun bayan kafa shi da aka yi.
Asase ya jaddada cewar daga cikin nasarorin da wannan kwamiti da yake jagoranta ya samu akwai rufe guraren da ake shirya fina-finai ba bisa ka’ida ba har guda 3 tare da kama Daraktoci 2 da sauran ma’aikata da jaruman masana’antar ta kannywood har 32 wanda a cewarsa hakan wata babbar nasara ce ga masana’antar ta kannywood.
- Kamfani Ya Maka Bankin Globus A Kotu A Kan Karya Yarjejeniyar Bashi
- Lallai A Hukunta Waɗanda Suka Kai Mamaya Ofishin NLC – TUC
Malam Tijjani Asase ya bayyana hakan ne ga Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano Alh Abba El-mustapha yayin da kwamitin yake bayyana wani bangare na rahoton wasu daga cikin nasarorin aiyukan da suka samu tun bayan nada su a matsayin shuwagabanni.
Da yake nasa jawabin Alh Abba El-mustapha ya jinjinawa shugaban kwamitin tare da membobinsa duba da yadda suka jajirce wajen sauke nauyin da hukumar ta dora musu duba da cancantarsu tare da kishin da suke da shi na ganin hukumar da masana’antar ta kannywood sun sami ci gaba mai dorewa.
Alhaji Abba El-mustapha ya jaddada cewa ba’a kafa kwamitin dan a ciwa kowa mutunci ba face tsaftacewa tareda fito da kima da daraja ta masana’antar kannywood a idon Duniya inda ya kara da cewa manufar kafa kwamitin ita ce tabbatar da ana bin doka da ka’ida a masana’antar kannywood sau da kafa tare da bin duk wata hanya da ake ganin masana’antar za ta samu cigaba da kuma cire gurbatattu da cikinsu wadanda suke janyo wa masana’antar zagi ta yadda zata yi gogayya da sauran takwarorinta na Nijeriya dama duniya baki daya.
Abba El-mustapha ya tabbatar da cewa tuni lokaci ya kure da wasu zasu ringa amfani da sunan masana’antar ta kannywood suna abinda bai kamata ba domin cimma kudurorin kashin kansu.