A wannan makon shafin Taskira zai yi tsokaci ne game da abin da ya shafi rayuwar matasa a yanzu, duba da wannan yanayi da ake ciki, dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin matasa; shin me ya fi damun matasa a yanzu? Mece ce mafita kuma ta wacce hanya za a shawo kan matsalar?
Ga dai bayanan nasu kamar haka: Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:
Matasa na fuskantar kalubalen rayuwa iri-iri musamman a halin da ake ciki a wannan rayuwar duba da yanayin, tare da canji da aka samu, abubuwa da dama na damun matasa a wannan kasar ta mu a cikin wannan kankanan lokacin, wadannan abubuwan sun hada da; rashin samun dama, matasa basu samun dama wadda ya kamata a ce sun samu a harkokin rayuwa na yau da kullum, a inda za ka ga cewa a gurare da dama an toshesu ko in ce a kan ki ba su dama yadda ya kamata domin gudanar da abubuwan da ya dace.
Na biyu yunwa da talauci, wanda idan aka yi la’akari da hali tare da yanayin da ake ciki a yanzu kudin da matashi zai yi amfani da shi domin cin abinci sau uku a rana a yanzu ba zai masa ba, koda wajen samin abinci ya kan samu na lokaci daya a rana. Na uku rashin aikin yi, a halin da ake ciki a yanzu a kasar nan tamu za ka iya samun matashi wanda ya shekara sama da goma ba tare da aikin yi ba koma sama da haka, kuma yayi karatu, sannan na da ilimi hadi da dubarun aiki. Na hudu rashin wadataccen ilimi, matasan mu a yanzu da yawa za ka samu babu wadataccen ilimi sakamakon rashin samun dama, talauci da dai sauran abubuwa da makamantansu.
Na biyar rashin zaman lafiya na daya daga cikin abubuwan dake damun matasa sakamakon toshewar hanyoyi samun su tare da sa musu tsoro wajen fita tare da fafutukar neman kudi da neman mafita wanda sanadiyyar hakan ya sa matasa da dama sun sarewa rayuwa tare da karbar zaman talauci da babu. Na shida sonkai ko wariya ga matasa, matasa da dama suna damuwa da irin sonkan da ake nunawa a kansu musamman wani lokacin za ka ga cewa an fi bawa mata dama sama da matasa maza, wanda hakan na sawa a kasa katabus a abubuwa da dama na cigaban rayuwa duba da la’akari da karfin tunanin mata da na maza ba daya bane ba musamman wajen yin jagoranci da yanke hukunci, a wasu lokutan kuma za ka ga matasan da ake bawa damar bai kamata a ce an basu ba saboda rashin cancantarsu amma za ka ga an basu saboda sonrai da son zuciya wanda hakan za ka ga na taba ma matasa zuciya matuka wanda yake sa su cikin damuwa, rashin ingantacciyar lafiya matasa na fuskantar damuwa a lafiyar su sakamakon rashin samun abinci maigina jiki, rashin motsa jiki, fama da aikin karfi dama amfani da miyagun kwayoyin wanda duka abubuwa ne da ka iya damun lafiyar matashi tare da haifar masa jinya iri-iri.
Na farko ya kamata gwabnati ta samawa matasa aikin yi tare da kirkiro wasu hanyoyin domin bawa matasa jari da za su dogara da kansu a rayuwarsu ta yau da kullum, na biyu taimakawa matasa wajen samun ingantaccen ilimi ta hanyar daukar nauyin karatunsu a makarantu, tare da samar da kayan koyo da koyarwar na zamani daga gwabnati, basu taimakon kudi domin gudanar da karatunsu don biyawa kai bukata na yau da kullum dama yin amfani da kudin don abubuwan da ka iya bujirowa, a harkokin karatunsu, fitar da matasa masu hazaka kasar waje domin koyon fikirori tare da samun ilimi daga wajen turawa musamman a bagaren abubuwan da suka shafi kere-kere da kir-kira, na uku ya kamata ‘yan siyasa suna bawa matasa dama tare da daina sako sonrai, sonkai, wariya, cin hanci da rashawa, a cikin harkokin gudanar da mulkinsu musamman a bangarori abubuwa da suka shafi cigaban matasa domin bawa wanda suka kamata da wanda suka dace dama a matsayinsu na shuwagabbannin kuma jagorori, samar da masana’antu da gina-ginan kamfaninnika a kauyuka daga gwabnati da masu kudi da ‘yan kasuwa domin bawa matasa damar samun aikin yi da cigaban rayuwar su da kuma habaka kasuwaci tare da tattalin arzikin kasar mu.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, Jos Jihar Filato:
A bai wa matasa damar ba da gudunmawa.
Babu shakka bisa ga abubuwan da ke faruwa a kasar nan ya nuna cewa matasa suna bukatar samun damar da za su ba da gudunmawa don a bangarorin rayuwa daban-daban. Suna bukatar a rika damawa da su, ana sauraron shawarwarinsu, ana sa su cikin hidimar tafiyar da harkokin gwamnati bisa cancanta da dacewa, ba sai don sun fito daga wani babban gida, ko suna da alaka da babban jami’in gwamnati ko dansiyasa ba. Cin hanci da rashawa da yake addabar kasar nan yana hana matasa da dama samun ‘yanci da damar da suke bukata don cigaban rayuwarsu. Sai dai kamar yadda ba zai yiwu a samu canji a lokaci guda ba, haka su ma matasa ya kamata su gane ba a kwatar ‘yanci ko dama da karfin tsiya, dole sai an bi matakan da suka dace, an yi karatu, an samu gogewa, an yi hakuri, an yi biyayya, sannan za a cimma abin da ake muradi na rayuwa. Lallai ne dattijan kasar nan su gane lokaci ya yi da za su koma gefe su bai wa matasa dama su ma su nuna irin tasu basirar da baiwar da Allah Ya basu.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri, A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya matsalolin da suke damun matasa ko addabar su a wannan lokaci sunada yawa to, amma uwa’uba shi ne rashin aikin yi, kuma gashi mun samu kan mu a cikin yanayi na matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa wanda hakan ya kara tabarbarewar al’amarun matasa, musamman ta fuskar samun aikin yi domin dogaro da kai.Hakika akwai matsalar shaye-shaye ita ma tana daga cikin matsalolin matasa a wannan lokaci. To, mafita guda daya ce gwamnati ta dauki matakin samar da ayyukan dogaro da kai domin matasa su samu sana’oi da za su shagaltar da su domin kaucewa fadawa ayyukan daba ma sace-sacen kayan al’umma, hakika wannan matsalar rashin aikin yi na daya daga cikin abun da ya addabi kasar mu Najeriya a yau. To, shawara ta ni dai ita ce gwamnatin kasar mu Najeriya tayi kokarin samarwa da matasa makarantun koyar da sana’oi domin hakan zai taimaka sosai wajen rage zaman banza, kuma ya kamata gwamnati ta gayyato kamfanoni masu zaman kansu domin samawa matasa aikin yi wanda hakan zai taimaka wajen rage dogaro da gwamnati, hakika mafi yawan matasa sun dogara ne da aikin gwamnati shi ne ya jawo suke zaman kashe wando. Daga karshe nake addu’ar Allah ya kawo mana karshen wannan matsala, Allah yayi riko da hannayen shugabanin mu wajen magance wannan matsala da ta addabi kasar mu.
Sunana Fatima Tanimu Ingawa Daga Jihar Katsina:
Babbar damuwar matasa a wannan yanayi da ake ciki na yanzu bai wuce rashin aikin yi ba, rashin aikin yi kama daga aikin gwamnati dama aikin masana’antu ko aikin hannu. Wanda shi ke jaza fatara da rashi ga matasa dama wadanda suka dogara da su. Na farko dai aikin gwamnati ya yi wahalar gaske ga samuwa, sannan ba mu da wadatattun masana’antu da kamfanoni da za su rage mana radadin talaucin da ake fama a wannan rayuwa. Sannan kuma aikin hannun ma babu wani wadatten jarin da mutum zai fara da shi. Aikin hannun ma a wannan rayuwar sai na tilas kadai ke shiga don mutane yanzu bakin ciki kawai ake, kayan abinci da ya zama dole ga bawa shi ake saye ba wani sauran ababen more rayuwa ba ga dai masu karamin karfi. Babbar mafita ita ce a koma ga Allah, a gyara halaye da dabi’a, a kuma rike gaskiya da amana.
Sunana Saudiboi Daga Saudiya
Shawarar da zan bawa matasa na Nageriya gabadaya ba ‘yan kudu ba, ba ‘yan Arewa ba kowa, abu daya biyu zuwa uku ne, na farko; Ka tashi ka nema, a nemi abin da za a yi, ba lallai sai an nemi aikin gwamnati ba ko leburanci ne ko saran itace ne, ko kauyenku ne ka je ka nemi abin da za ka dan nema wanda za ka zo ka dan kafa kanka, ana harkar noma, kanada kauyen mama da babaka samu ka dan lallaba. Shawo matsala dole sai mutum ya fara rike kansa ka fita daga harkar duk wannan ‘yansiya-siyar ka fita daga harkarsu, ba ruwanku da wannan zabe-zaben shurmen, domin zaben ko kun zaba ko baku zaba ba shurme yake kawo muku.
Sunana Ibrahim Danmulky, Daga Unguwar Gama Brigade Jiihar Kano:
A wannan hali da ake ciki a yanzu abin da ya fi damun matasa bai wuce rashin kudi ba, gashi kuma gari ya tsaya cak! babu wata hanya da kudi yake shigomusu balle su biyawa kansu bukatu wanda ya jawo wasu da yawan matasan sun fada wani mummunan yanayi marar misaltuwa. Mafita guda 2 ne na farko gwamnati da iyayen matasan su kirkiri wata hanya don wayarwa da matasa kai kuma kada ta gaji da wayar musu da kan, hanya ta biyu gwamnati ta sake kirkirar wasu damammaki na aiki, sannan su sauaaka damar ga wadanda suka yi karatu a cikin matasan dama wadanda basu yi ba. Shawarata bai wuce in ce mu ji tsoron Allah sannan mu yi amfani da damar da ya bamu kafin ta kubce mana ba, idan yau mu matasane watarana masauka ne, mu gyara tunaninmu mu amfani lokaci don cin moriyar gobe.
Sunana Hafsat Sa’eed Daga Jihar Neja
A yanzu abin da ya fi damun matasa matsalar rashin aikin yi da kuma fama da tsadar rayuwa tare da abin da za a ci. Babu wata mafita face mu mika lamarinmu zuwa ga Allah, dan shi kadai zai iya magancewa a halin da ake ciki yanzu.
Sunana Lawan Isama’il (Lisary), Daga Jihar Kano; Rano:
Matsin tattalin arziki da rashin tsaro a wasu sassan kasar nan da rashin ayyukan yi duk da akwai dubban matasa sun yi karatu mai nisa amma suna zaune haka siddan. Babbar mafita a kan wadannan shi ne; mu yi addu’a, sannan mu gyara halayen mu duba da ni ina aikata laifi kai ma kana yi wancan yanayi ke kina yi waccar tana yi to, sai mu hadu kowa ya gyara nasa lefin, sannan su ma shuwagabanni su duba Allah su duba ma’aiki su yi wa talakawan dake a kasansu abin da ya dace dasu tunda ai duk wani shugaba ya san halin da talaka yake a ciki tunda ai idan shi bai taso cikin talaka ba amma kafin ya zama shugaba ya za ga ya ga halin da talakan yake a ciki. Shawarata ga matasan mu masu tasowa a nan ita ce; mu rage buri, mu daia raina sana’a, sannan mu dogara ga Allah kuma mu tashi mu nemi na kanmu kada mu yi gadarar muna da kwalin karatun abu ka-za ko kuma na san wane a siyasance ko na san me kudi wane don haka sune za su taimaka min a’a! mutsaya mu nemi na kanmu sannan mu gyara halayenmu muna addu’a kuma. Allah ya sa mu dace, amin.
Sunana Hassana Sulaiman Hadejia, A Jihar Jigawa:
Abin da ya fi damun matasa a yanzu bai wuce tsadar rayuwa ba, da rashin inganta musu ayyukan da suke gudanarwa na yau da kullum ba. Mafita a nan ita ce kawai a inganta rayuwarsu a sama musu ayyukan yi ,a kuma basu damar shiga cikin gwamnati ana damawa da su sannan kuma wadanda suke da fasahar kirkira ana daukar nauyin karatun su zuwa kasashen waje dan samun horon da idan sun dawo gida za su kafa wasu wuraren da za su na bawa sauran ‘yan uwansu horo da haka za a rage zaman banza a kuma kara masu ayyukan yi a kasa. Shawarar da za a bawa matasa cikin wannan kadamin da muka tsinci kanmu cikinsa shi ne matasa su tsaya su yi wa kansu karatun ta nutsu, sannan kuma su zama masu manufa a rayuwar su, su kuma kasance wadanda kannansu idan sun taso za su iya bugar ƙirji su yi alfahari da su a gobensu, matasa su tsaya tsayin daka wajen ganin sun samarwa da kansu ayyukan da za su na dogaro da su, sannan kuma su zama masu daina rakiyar ‘yan siyasa yayin neman zabe suna maida hankali wajen ganin sun samarwa da kansu wakilai nagari.
Sunana Muhammad Isah Zareku Miga A Jihar Jigawa
Wato magana ta gaskiya abun da ya fi damun matasa a halin yanzu shi ne rashin amintattun shugabanni. Na biyu gwabnati ba ta son damawa da su a harkar shugabanci. Sannan kuma matsatsin rayuwa a halin yanzu za ka ga matashi yana son taimakawa iyayensa, ‘yan’uwansa, dama sauran jama’a amma babu dama. Mafita a nan ita ce; matashi ya dage da neman na kansa wato jari na sana’a komin kankantarsa sannan kuma sai neman ilimin addini da na zamani kai har ma na sana’a. Shawara a:nan shi ne gwamnati tana bawa matasa ilimi mai rahusa sannan masu hannu da shuni suma suna taimakawa matasa bayan haka ‘yan kasuwa suna jan matasa a jika don koya musu sana’ar dogaro da kai.
Sunana Sa’adu Abdullahi Inuwa Malam Madori A Jihar Jigawa:
A halin yanzu abin da ya fi damunmu mu matasa shi ne rashin abin da za mu dogara da kanmu, domin wallahi rayuwar matasa tana cikin wani hali a wannan lokacin domin ba mu da abin yi wanda za mu samu kudi wadda har za mu iya biyawa kanmu bukatu balle mu taimakawa iyayenmu. A wannan lokacin da muke ciki mafita daya ce a samawa matasa aikin yi da kuma basu jari domin su fara kasuwa domin dogara da kansu. Sannan kuma gwamnati ta cigaba da kirkirar makaratun koyan sana’o’in hannu domin koyawa yaran da suka taso sana’a tun suna kanana domin su taso da shi dan Inganta rayuwarsu. Ina mai bawa ‘yan’uwana matasa shawara da su tashi tsaye domin neman na kansu kada su dogara da gwamnati sai ta basu aikin gwamnati mu tashi mu nemi sana’a duk kankantarta. Ina sake bawa matasa shawara da kada su dogara da ‘yan siyasa wajen maida su hanyar neman abincin su domin siyasa ba sana’a ba ce, mu tashi mu nemi sana’a duk yadda za a yi domin mu taimaki ‘yan’uwanmu.
Sunana Aishat D. Sulaiman, Daga Gombe:
Abin da ya fi damun marasa tsadar abinci, dan shi ya fi dagawa kowa hankali a yanzu babba da yaro, tsoho da tsohuwa, wanda hakan ya janyo kudin da ake samu karancinsa bai kai ka sayi abincin da za ka ci a wuni me iyali ba. Shawo kan wannan matsala tana ga shuwagabanni yana ga mu, sabida a kanmu muna yi wa juna bakin ciki da hassada da kyashi, talaka yana kin dan’uwansa talaka, talaka zai ga dan’uwansa a cikin wani hali na jarrabawa ba kowa ne Allah yake bashi ikon taimakonsa ba, kun ga kenan mu ya mu ma munada matsala, idan aka tsarkake zukata aka taimaki juna in sha Allahu Allah zai taimake mu.
Sunana Hamza Rabiu Malam Madori (Abba Alhaji):
A wannan halin da ake ciki matasa a wannan kasar tamu ta najeriya matasa suna cikin wani hali na talauci da rashin aikin yi da kuma karancin ingantaccen ilimi wanda za su yi amfani da shi wajen mu’amala ta yau da gobe, baya ga haka matasa a wannan lokacin suna fama da rashin zuciya wajen neman na kansu saboda sun dogara da gwamnati sai ta basu aikin yi wanda suna kwance ko suna ofis albashi yana shigo musu ko wani alawus bayan Allah ya azurta mu da lafiya da kuma tattalin arziki a wannan kasar tamu ta najeriya muna da filaye da za mu yi amfani da su wajen yin noman tudu ko na kwari a wannan lokacin da muke ciki iya noma da kiwo kadai matashi ya dogara da shi zai iya rayuwa ba sai wata gwamnati ta bashi aiki ba. Mafita a wannan kasar ta nijerya ya kamata mu dukufa wajen yi wa kasar mu Addu’ar Allah zamar da lafiya bayan haka yaka mata jama’a mu tsaya mu yi karatun ta nutsu muduba rayuwar da ‘yan’uwan mu talakawa suke ciki mafita ita ce su kansu ‘yan kasuwa su tsaya ga Allah a daidai ta farashin kayan masarufi a halin da ake ciki yanzu za ka je shago ka siyi kaya amma kana komawa sai ka ga farashin kayan ya karu kuma wannan kayan ba wani a ka saro ba wancen na bayan ne da aka siyar maka baya ga haka ita ma gwamnati ya kamata ta yi amfani da tattalin arzikin da yake kasar nan tamu wajen shigo da abinci a siyar musu a farashin Mai sauki hakan zai saka ‘yan kasuwa su rage sai saita farashin kayan masarufi a wannan kasar.