Mataimakiyar shugaban kasar Amurka kuma ‘yar takarar shugabancin kasar a jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, ta bayyana cewar kasar na yin duk mai yiwuwa don ganin an tsagaita wuta a yakin da ake yi a gabas ta tsakiya.
Ta bayyana haka ne yayin wata tattaunawa ta musamman da gidan talabijin na CBS, gabanin zaben shugaban kasa a wata mai zuwa.
Ta kare kokarin gwamnatin shugaba Biden na hana barkewar yaki a gabas ta tsakiya, duk da cewa Isra’ila na ci gaba da yin shuri da bukatar Amurkar na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Ta ce “Ba za mu taba gajiyawa wajen neman ganin bukatar Amurka ta neman ganin yakin nan ya zo karshe ta biya ba.”
Ta kuma amsa tambayoyi kan tattalin arziki, shige da fice da batun yakin Ukraine.
A makon da ya gabata ne, gidan talabijin na CBS ya sanar da cewa abokin hamayyarta na jam’iyyar Republican, Donald Trump, ya janye daga tattaunawar, ba tare da bayar da wani dalili ba.
Duk da haka manyan ‘yan takarar biyu na ci gaba da caccakar juna a wuraren yakin neman zabe da kuma kafafen watsa labarai.